Trump Zai Yi Maraba Da Tawagar Kasar Iran A Gasar Kofin Duniya —Infantino
[ad_1]
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce kasar za ta yi maraba da tawagar kasar Iran yayin da za ta karbi bakuncin gasar Kofin Duniya da za a buga a wannan shekarar a kasashen Amurka, Medico da Canada duk da cewa kasashen suna cikin yaki, a cewar shugaban FIFA Gianni Infantino.
A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Instagram, Infantino ya ce ya gana da Trump a ranar Talata domin tattauna shirye-shiryen gasar, wadda Amurka, Canada da Medico za su karbi bakunci, kuma za a fara a ranar 11 ga Yuni.
- Tinubu Ya Kaddamar Da Shirin Aikin Noma Domin Samar Da Wadataccen Abinci
- Duniya Ta Shaida Kokarin Sin Bisa Shirin Ci Gaban Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’Umma Na Shekaru Biyar-Biyar Karo Na 15
Infantino ya ce shi da Trump sun yi magana game da halin da ake ciki a Iran, an shirya Iran za ta buga wasanni uku a Amurka, amma yanzu ana shakku kan halartarsu kasar, tun lokacin da Amurka da Isra’ila suka fara yaki a tsakaninsu, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar Shugaban Addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei.
Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki zuwa Isra’ila da kasashe hudu na yankin Gulf wadanda ke karbar bakuncin sansanonin sojin Amurka da suka hada da Bahrain, Kuwait, Katar da Hadaddiyar Daular Larabawa.
A yayin tattaunawar, shugaba Trump ya sake nanata cewa, “Ba shakka, kasar Amurka tana maraba da tawagar Iran” in ji Infantino, Iran za ta fafata da New Zealand da Belgium a Los Angeles a ranakun 15 da 21 ga watan Yuni kafin ta buga da kasar Masar a Seattle a ranar 26 ga watan na Yuni.
A makon da ya gabata Trump ya shaida wa jaridar Politico, cewa “Gaskiya ban damu ba idan Iran ta buga gasar cin kofin duniya a kasar nan” bayan fara yaki tsakanin kasashen, an ambato shugaban hukumar kwallon kafa ta Iran Mehdi Taj yana cewa “Abin da ya tabbata shi ne bayan wadannan hare-haren, yana da wuya muyi marmarin zuwa Amurka”.
[ad_2]
Source link