Jarumin Kannywood Umar Ascon ya rasu a Kano
[ad_1]
Allah Ya yi wa jarumin fina-finan Hausa Umar Ascon, wanda aka fi sani da Alhaji Lado Mai Barkono a cikin shirin nan mai dogon zango Garwashi, rasuwa.
Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ne a Asibitin Koyarwa ma Malam Aminu Kano, bayan ya shafe lokaci yana fama da rashin lafiya.
Wani furodusa a masana’antar Kannywood, Abubakar Yahaya Matinko, wanda suke unguwa ɗaya da marigayin, ya tabbatar da rasuwar jarumin.
Ya ce ko da yake marigayin bai daɗe a masana’antar ba, amma cikin ƙanƙanin lokaci ya samu karɓuwa sosai a wajen masu kallo.
Ya ƙara da cewa marigayin ya rasu ya bar mata ɗaya mai juna biyu da kuma ’ya’ya mata biyu.
Kafin shigarsa harkar fina-finan Hausa, marigayin yana kasuwancin man fetur a Hotoro Depot a Kano.
Daga baya ne ya shiga harkar fim inda ya zama ɗaya daga cikin jaruman da suka yi fice a cikin shirin Garwashi a matsayin Alhaji Lado Mai Barkono.
Baya ga haka, ya fito a wasu fina-finan Hausa kamar Wata Shida, Manyan Mata da sauran su.
An gudanar da jana’izarsa a Masallacin Al‑Masjlisul Islami da ke unguwar Hotoro Ring Road a Kano, kusa da gidan man Gade-Gade, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Tuni jarumai da masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood suka fara miƙa saƙon ta’aziyya tare da nuna alhininsu kan rasuwar jarumin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link