An Samu Karuwar Tafiye-Tafiye Tsakanin Yankunan Sin Yayin Bikin Bazara Na Bana
[ad_1]
Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin, ta ce an samu karin yawan tafiye-tafiye tsakanin yankuna daban daban na Sin, yayin balaguron lokacin bikin bazara na bana, wanda a kan kira “Chunyun” da harshen Sinanci.
Alkaluman da ma’aikatar ta fitar a Asabar din nan, sun nuna cewa, a kwanaki 40 na karuwar balaguro da Sinawa ke ki tsakanin sassan kasar, a bana irin wadannan tafiye-tafiye sun kai biliyan 9.41. Adadin da ya karu da kaso 4.3 bisa dari kan na lokacin bikin bazarar shekarar 2025. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link