Dalilin Da Ya Sa Taraba Ba Za Ta Samu Amfanin Gona  Mai Yalwa Ba A 2026

[ad_1]

Wani bincike da jaridar LEADERSHIP ta gudanar, ya nuna cewa; kudin shigar da sashen bayar da hayar taraktocin noma na Jihar Taraba, wato THU ke son samu a 2026 na hayar taraktocin noma, ba za su samu kamar yadda suka tsara ba.

Hakan zai kasance ne, sakamakon ganin cewa; taraktocin noma biyu kacal ne, na Cabrio aka ware wa sashen, wanda hakan ya nuna cewa; sun yi matukar karanci a aikin noman da za a yi a kakar aikin noma ta 2026.

  • Kasar Sin Na Da Kayayyakin Tarihi Na Halittu Na Duniya Guda 15
  • Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku A Saudiyya

Ana dai sa ran sashen, zai samar da kayan aikin noma da ake bukata, domin a samu tumbatsar amfanin gona, bayan an samu taraktocin noma, inda tuni manoman jihar, suka fitar da tsammanin samun wani amfanin gona mai yawa.

Binciken ya kuma nuna cewa, akalla sashen na bukatar a samar masa da taraktocin noma guda 35, da suka hada da guda biyun da aka samar na Cabrio, domin yin noma a 2026.

Idan za a iya tunawa, gwamnatin jihar ta Taraba, ta kirkiro da sashen ne, domin samar da kayan aikin noma ga manoman da ke jihar a cikin farashi mai sauki, musamman domin inganta rayuwar al’ummar jihar da kuma kara samar da kudaden shiga.

Kazalika, an kirkiro da sashen ne, domin a rika horas da injiniyoyi da rabar da taraktocin noma ga kananan hukumomin jihar 16 da kuma wasu sassa biyu, wadanda suka kasance, sun dakile ayyukan ma’aikatar bunkasa aikin noma da samar da wadataccen abinci.

Jim kadan bayan karbar taraktocin noman daga wurin ma’aikatar bunkasa aikin noma da samar da wadataccen abinci ta jihar, Janar Manaja na hukumar, Injiniya Danladi Shatalis, ya yi godiya ga gwamnan jihar Agbu Kefas, kan kokarin da gwamnatinsa ke ci gaba da yi na farfado da fannin aikin noma na jihar.

Injiniya Shatalis, ya kuma yaba da shirin da aka kirkiro da shi na samar da taraktocin noma, musamman domin samar da kayan aikin noma na zamani da kara habaka samar da wadataccen abinci a jihar.

Kazalika, ya gode wa kwamishinan ma’aikatar, bunkasa aikin noma da samar da wadataccen abinci na jihar, Farfesa Nicholas Oliber, kan ci gaba da taimaka wa sashen, musamaman kan samar da taraktocin noma guda biyu da kuma wasu kannan taraktocin noma, duk da bukatar da sashen ya gabatar na bukatar manyan taraktocin noman, domin cimma bukatar da manoman jihar suke da ita.

Bugu da kari, ya yaba wa shugaban kwamtin kula da bunkasa aikin noma da samar da wadataccen abinci na jihar, na Majalisar Dokokin Jihar, Hon. Abubakar Tanko Yusuf, kan goyon bayan da yake ci gaba da bai wa sashen, musamman goyon bayan da ya bai wa sashen a lokacin kare kashe kudin da aka ware wa sashen.

Duk da irin wannan yabo da kwamitin na Majalisar Dokokin ya yi wa sashen, sashen ya gaza cimma bukatar da ake da ita, na tara kudaden shiga a 2025, wanda hakan ya nuna cewa; akwai bukatar a kara samar da taraktocin noma ga sashen, musamman domin kara wadata jihar da abinci.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *