Shugabannin ECOWAS Sun Jaddada Aniyarsu Ta Yaki Da Ta’addanci
Shugabannin Kasashen Ghana, Laberiya da Saliyo tare da wakilai daga Burkina Faso, Mali, Mauritaniya, Nijeriya, Senegal da Togo, sun jaddada aniyarsu ta zurfafa hadin gwiwar kasashen yankin, wajen yaki da ta’addanci da rashin tsaro.
Shugabannin, sun gana a birnin Akara daga ranar 29 zuwa 30 ga watan Janairu, a wani babban taron bayar da shawara kan hadin kai da tsaro a yankin, wanda shugaban Kasar Ghana, John Dramani Mahama ya jagoranta, tare da Shugaban Kasar Saliyo, Julius Maada Bio da Shugaban Kasar Laberiya, Joseph Boakai da suka jagoranci tawagarsu.
- HOTUNA: Ɗan Ganduje Ya Ziyarci Kwankwaso A Kano
- Sinawa Masu Amfani Da Yanar Gizo Sun Kai Biliyan 1.125
A cikin sanarwar hadin gwiwar da aka fitar a karshen taron na kwanaki biyu, shugabannin sun yi gargadin cewa, yammacin Afirka ya zama wata cibiyar ta’addanci da tsattsauran ra’ayi a duniya, tare da yin nuni da cewa, “a kowace rana, ana samun hare-haren ta’addanci akalla takwas, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 44.
“Fiye da rabin duk mace-macen da ake samu, wadada ke da alaka da ta’addanci a duniya, ana samun su ne a yankunanmu. Muna ganin yadda ake samun tashin hankali a hare-haren masu tsattsauran ra’ayi, wanda rashin daukar mataki ba zai taba haifar mana da da mai ido ba.”
Taron, wanda ya biyo bayan shawarwarin da ministocin harkokin waje da na jami’an tsaro da leken asiri suka yi, ya kuma samu nakaltowa daga Hukumar Tarayyar Afirka, shirin raya ci gaban Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyoyin fararen hula.
Sanarwar ta jaddada bukatar samar da wani tsari na dindindin na hadin gwiwa, wanda zai wuce “diflomasiya ta al’ada ko iyakanceccen aiki.”
Ya kara da cewa, tsarin zai mayar da hankali a kan shirye-shiryen da aka tanada da ka’idoji da kuma sauran abubuwan more rayuwa.
A game da yaki da ta’addanci, shugabannin sun amince da “karfafa tarukan yau da kullum na jihohi a yankin, domin sake duba alkawuran zaman lafiya da tsaro,” inganta musayar bayanan sirri, daidaita tsarin shari’a, don gurfanar da laifuffukan da ke da alaka da ta’addanci da kuma karfafa shirye-shiryen kawar da tsattsauran ra’ayi.
Domin magance tsaron kan iyaka, taron ya himmatu wajen yin la’akari da daukar yarjejeniyoyin “zafafa bi”, da tsara ka’idar fahimtar juna a cikin watanni uku da karfafa hanyoyin yaki da fataucin miyagun kwayoyi da makamai. Yarda da cewa, martanin soji kadai ba zai iya tabbatar da zaman lafiya mai dorewa ba, sanarwar ta yi alkawarin bayar da fifiko ga tsaron lafiyar mutane ta hanyar samar da abinci, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi da kuma ilimi.
Har ila yau, ta yi kira da a karfafa gudanar da mulki a cikin gida da kuma amfani da fasahar zamani, domin zamanantar da sarrafa kan iyakoki da sauran ayyuka.