Sin Za Ta CI Gaba Da Ba Da Damar More Babbar Kasuwarta Ga Duniya A Wannan Shekara
[ad_1]
An gudanar da taron farko na shekara ta 2026 na “raba cin gajiyar babbar kasuwa ga duniya: kawo kayayyaki kasar Sin ” a ran 4 ga watan. Yayin taron, mataimakiyar shugaban Tesla Tao Lin ta ce, wannan aikin ba wai kawai wata alama ce a fili ta yadda Sin ke fadada bude kasuwarta mai zurfi ga duniya ba, ” har ma ya kawo damammaki mafi muhimmanci da ba a taba ganin irinsa ba ga kamfanoni masu jarin waje ciki har da Tesla”.
A matsayinta na kasa mafi girma a duniya a bangaren cinikin kayayyaki, Sin tana dora matukar muhimmanci kan fadada shigo da kayayyaki daga ketare, kuma ta ci gaba da zama kasuwar shigo da kayayyaki ta biyu a duniya na tsawon shekaru 17 a jere. Bukatun Sinawa na ingantattun kayayyaki da hidimomi za su ci gaba da fadada, duba da yadda take fara aiwatar da shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shakaru biyar-biyar karo na 15, kasuwar Sin na da matukar boyayyen karfin sayayya da tarin damammakin shigo da kayayyaki daga ketare.
A shekarar farko da aiwatar da shirin karo na 15, Sin ta kaddamar da jerin ayyuka masu taken “raba cin gajiyar babbar kasuwarta: kawo kayayyaki kasar Sin “, ainihin matakin dake bude kasuwarta ga duniya da kuma samun daidaito tsakanin shigowa da fitar da kayayyaki. Wanda zai yi hadin kai da CIIE don samar da karin hanyoyin shigo da kayayyakin duniya zuwa kasuwar Sin.
Matakin ba kawai yana samar wa Sinawa da zabin sayayya iri-iri ba ne don biya bukatun cikin gidan kasar Sin, yana kuma samar wa kamfanoni masu jarin waje ingantaccen dandali na hadin gwiwa don more damar “fitar da kayayyakinsu zuwa Sin”. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link