‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’
[ad_1]
Amina Hassan, matar Yakubu Makuku, mai gadin makarantar ’yan mata ta GCGSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi, wadda aka kai wa hari da safiyar Litinin, ta bayyana yadda aka kashe mijinta.
Da take magana da ’yan jarida a wurin da lamarin ya faru, ta ce bayan da maharan suka kutsa cikin makarantar, sai suka shigo cikin gidansu.
Matar ta ce ba ta san cewa mutane ne a bakin ƙofar ba sai da suka shigo cikin ɗakinsu.
“Da misalin ƙarfe 4:00 na Asuba a ranar Litinin muna kwance ni da mijina sai muka ji ana ƙoƙarin karya ƙofar dakinm. Na tashe shi amma ya yi tunanin akuya ce ke motsi a waje.
“Kafin mu ankara, sai gungun ’yan bindiga suka shigo ɗakinmu suka ce ya kai su ɗakin kwanan dalibai. Da ya ƙi, sai suka harbe shi. Na yi gaggawar rungumarsa, amma suka ture ni gefe suka ci gaba tafiya ɗakin daliban.
“Ban san yadda suka yi suka sace ’yan mata ba, amma na ji ihunsu da kukansu. Har yanzu abin yana min kamar mafarki mai ban tsoro,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa wani mutum mai suna Ali Shehu, wanda shi ne mai gadin makarantar, shi ma ’yan bindigar sun harbe shi har lahira.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link