Ana Hasashen Haihuwar Jarirai Har 700,000 Cikin 2026 A Kano

[ad_1]

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ana sa ran jihar za ta samu haihuwar jarirai tsakanin 600,000 zuwa 700,000 a shekarar 2026, lamarin da ta ce na iya ƙara matsin lamba ga tsarin kiwon lafiya na jihar.

Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ne ya bayyana hakan a ƙarshen mako yayin bikin karramawar ɗalibai na farko na Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da Fasaha ta Sardauna da aka gudanar a Kano.

  • Ganduje Ya Koma Abuja Daga Landan, APC Na Shirye-shiryen Karɓar Gwamnan Kano
  • Gwamna Yusuf: “Allah Ne Ya Sanya Ni Gwamna, Muradun Kano Ne Gaba, Ba Biyayya Ga Wani Ba”

Dakta Nagoda ya ce an samo wannan hasashe ne bisa ƙididdigar ƙaruwa a yawan jama’a daga ƙidayar 2006, wadda ta nuna cewa yawan jama’ar Kano na ƙaruwa da kusan kashi 3.5 cikin ɗari a kowace shekara. Ya ƙara da cewa wannan ƙaruwa na ci gaba da zarce adadin ma’aikatan lafiya da kuma kayayyakin more rayuwa da ake da su a jihar.

Ya bayyana cewa Kano na fuskantar ƙarancin kusan ma’aikatan lafiya ƙwararru 4,000 a halin yanzu, yana mai gargaɗi cewa yawaitar haihuwa da ake sa ran samu na iya ƙara tsananta wannan giɓi tare da shafar ingancin ayyukan asibitocin gwamnati.

Dangane da gina ƙwarewa ma’aikata, Dakta Nagoda ya yi kira ga cibiyoyin horas da ma’aikatan lafiya da su ƙarfafa ɓangaren aikace-aikacen koyarwa (practical), domin tabbatar da cewa waɗanda suka kammala karatu sun shirya tsaf don yin aiki ga al’umma. Ya kuma bayyana cewa gwamnati na shirin ɗaukar ƙarin ma’aikatan lafiya tare da mayar da hankali wajen tura su zuwa yankunan da ke da ƙarancin samun kulawar lafiya, ciki har da Doguwa, da Rogo da Sumaila.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *