Za mu aiwatar da dokar takaita kashe kudin aure

[ad_1]



Gwamnan Sakkwato Ahmed Aliyu ya sanar cewa nan ba da jimawa ba gwamnatinsa za ta fara aiwatar da dokar hana kashe kudi fiye da kima a harkokin aure a jihar.

Da yake bude Masallacin Zawiyya Sheikh Aliyu Bunza da makarantar Islmaiyya a Sakkwato, gwamnan ya ce, “Nan ba da dadewa ba za mu zauna da masu ruwa da tsaki a jiha domin sake duba dokar hana kashe kudi fiye da kima ga harkokin aure a jiha.”

Ya bayyana cewa daukar matakin ya zama wajibi ne ganin yadda masu shirin aure suke shan wahala a harkoki kafin daurin aure, lamarin da ya ce ya kara sanya aure, ya yi wahala a tsakanin matasa mata da maza da suka kai lokacin yin aure.

A cewarsa kashe kudi fiye da kima almubazaranci ne da ke ba da gudunmuwa sosai wajen yawaitar tuzurai mata da maza.

Ya ce yawancin iyaye da magabata suna karya dokar takaita kashe kudin aure a jihar, inda suke yin almubazaranci a abubuwan da ba dole ba a yayin bukukuwan aure.

A cewarsa, saba dokar ya sa dole gwamnati ta shigo don tabbatar da abin doka yanda ya kamata.

Gwamnan ya ce albuzarancin ya taimaka wajen yawaitar halin rashin tarbiya a tsakanin matasa da suka kasa yin aure saboda tsadarsa ga abubuwan bukata da ake nema.

Gwamnan ya yi kira ga iyaye da magabata da malaman addini da sarakunan gargajiya su goyi bayan gwamnati a tabbatar da dokar ta yi aiki.

A watan Mayun shekarar 2023 ne Majalisar Dokokin Jihar Sakkawto ta amince da dokar hana almubazaranci a harkokin aure.

Kudurin dokar, dan majalisa Abubakar shehu Yabo da Faruku Mustafa Balle suka samar, ta hana almubazaranci a bukin aure, zanen suna da sauran bukukuwan al’ada.

Sama da shekara biyu da samar da dokar amma ba a aiwatar da ita a harkokin aure a jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *