Zargin Da Amurka Ta Yi Wa Sin Game Da Gwajin Nukiliya Ba Shi Da Tushe
[ad_1]
Zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD da ma sauran kungiyoyin kasashen duniya dake birnin Vienna, Li Song ya bayyana cewa, kasarsa na tsayawa tsayin daka wajen musanta zargin da kasar Amurka ta yi ma ta cewar, wai ta yi gwajin makaman nukiliya.
Li Song ya ce, kwanan baya, cikin taron shawarwari kan kwance damara da aka yi a birnin Geneva, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Amurka Thomas DiNanno ya yi zargin cewa, kasar Sin ta taba yin gwajin makamin nukiliya a watan Yunin shekarar 2020. Dangane da wannan batu, sakataren zartaswar sakatariyar kula da harkokin fasaha na kwamitin share fagen yarjejeniyar hana gwajin nukiliya bisa dukkan fannoni, Robert Floyd ya fidda sanarwa cewa, kungiyarsa ba ta taba ganin alamar aiwatar da gwajin nukiliya ba a wannan rana da kasar Amurka ta ambata. Hakan ya nuna cewa, zargin da kasar Amurka ta yi wa kasar Sin ba shi da tushe. Kana, wannan matakin da kasar Amurka ta dauka na rashin hankali ne, tare da nuna mugun burinta, da aniyarta ta farfado da gwajin nukiliya a kasarta, kuma kasar Sin ba za ta yarda da shi ba.
Bugu da kari, Li Song ya ce, tun daga shekarar 1996 da kasar Sin ta sanar da dakatar da gwajin nukiliya, ta cika alkawarinta a ko da yaushe, ba ta taba aiwatar da abun da ya saba wa wannan alkawari ba. Haka kuma, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen kare ra’ayi daya da kasashen duniya suka cimma na hana gwajin nukiliya, lamarin da ya sa, ta samu yabo daga gamayyar kasa da kasa. Amma, kasar Amurka ta bata sunan kasar Sin, da manufar nukiliyar kasar Sin, domin neman babakere ta fuskar ikon mallakar makaman nukiliya, da yin wasan siyasa domin kaucewa sauke nauyinta na kwance damara. Shi ya sa, za a iya cewa, kasar Amurka ita ce tushen bata tsarin nukiliyar kasashen duniya, da yanayin zaman karko na manyan tsare-tsaren duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
[ad_2]
Source link