Boko Haram ta wuce yadda mutane ke tsammani — Jonathan
[ad_1]
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce Boko Haram sun fi sojojin Najeriya makamai, lamarin da ya sa yaƙin ya zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin tsaron ƙasar nan.
Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin ƙaddamar da littafin Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya rubuta.
Jonathan, ya ce rikicin Boko Haram ya bambanta da sauran matsalolin da Najeriya ta fuskanta kamar na ’yan tawayen yankin Neja Delta da rikicin addini ko ƙabilanci.
Ya bayyana cewa Boko Haram sun samu goyon baya daga ƙasashen waje, suna da aƙidar tsattsauran ra’ayi da kuma makamai na zamani, abin da ya tsananta rikicin.
“Boko Haram ta fi yadda mutane ke tunani. A wani lokaci, mayaƙansu sun fi sojojinmu makamai, abin da ya nuna akwai ƙungiyoyin ƙasashen waje da ke tallafa musu,” in ji Jonathan.
Ya ƙara da cewa sace ’yan matan Chibok da suka yi a 2014 ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi baƙanta masa rai a lokacin shugabancinsa.
Jonathan ya kuma tuna yadda ya tunkari ’yan tawayen Neja Delta a lokacin da yake Mataimakin Shugaban Ƙasa.
Ya ce ya ziyarci sansanoninsu ba tare da tsaro ba, saboda ya yi imani cewa tattaunawa tare da amfani da ƙarfin soja ne zai kawo zaman lafiya.
Wannan dabara, a cewarsa, ta taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a yankin.
Amma ya jaddada cewar rikicin Boko Haram ya bambanta.
Ya ce idan son kawo ƙarshen Boko Haram, dole ne Najeriya ta haɗa matakan soja da kyakkyawan tsari shugabanci, rage talauci, tallafa wa matasa, da adalci.
“Ba za mu ɗauki Boko Haram kawai a matsayin matsalar tsaro ba. Tushenta talauci ne, da wariya. Sai an yi aiki gaba ɗaya kafin a samu zaman lafiya na gaskiya,” in ji shi.
Jonathan ya kuma yaba wa Janar Irabor bisa rubuta littafin, inda ya bayyana cewa zai taimaka wa al’umma su fahimci rikicin Boko Haram sosai, ya kuma zama jagora ga shugabannin gaba.
Taron ya samu halartar fitattun mutane ciki har da tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, tsohon Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Babagana Monguno, Hafsoshin Tsaro, Ministoci, Jakadu, da kuma Sarakunan Gargajiya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link