Shugaban Hukumar NAHCON Ya Yi Murabus Bayan Ƙorafe-ƙorafe A Kansa
[ad_1]
Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ya yi murabus daga muƙaminsa.
Leadership ta samu labarin cewa Farfesan ya ajiye aikinsa ne a daren ranar Litinin, a lokacin da hukumar ke shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana.
- Dalilin Da Ya Sa Gwamnan Bauchi Ya Sauke Kwamishinan Tsaron Cikin Gida
- ‘JAMB Ta Ce Laifi Ne Dalibi Ya Boye Matakin Karatun Da Yake’
Wani jami’i a hukumar ya ce murabus ɗin na da alaƙa da takardar ƙorafi da mambobin Majalisar Kwamishinonin NAHCON suka aike wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Takardar ta ƙunshi zargin aikata ba daidai ba a kan shugaban hukumar.
Jami’in ya bayyana cewa sakamakon wannan takarda ne Shugaban Ƙasa ya buƙaci Farfesa Abdullahi Usman Saleh ya ajiye aikinsa, musamman ganin yadda rigingimu da matsaloli suka addabi hukumar tun bayan naɗinsa.
Ya ƙara da cewa ana sa ran Fadar Shugaban Ƙasa za ta sanar da sunan sabon shugaban hukumar nan gaba kaɗan.
[ad_2]
Source link