Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar da Dakatar Da Sanata Natasha
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hallacin dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, inda ta bayyana cewa Majalisar Dattawa ta bi ƙa’idojin doka wajen ɗaukar matakin.
A hukuncin da alƙalan kotun uku suka yanke a ranar Litinin, kotun ta yi watsi da ƙarar da Sanatar ta shigar.
- An Gudanar Da Liyafar Murnar Bikin Bazara Na Sin Karo Na Farko A Zimbabwe
- Kasashe 10 Da Kudadensu Suka Fi Daraja A Duniya
Alƙalan sun bayyana cewa dakatarwar ba ta keta haƙƙinta na kundin tsarin mulki ba, kuma ba ta saɓa wa dokokin majalisar ba.
Sai dai, kotun ta soke tuhumar raini ga majalisa da kuma tarar Naira miliyan biyar da aka ɗora mata a baya, sakamakon wata wasiƙar neman afuwa da ta rubuta zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Hakazalika, kotun ta goyi bayan matakin Shugaban Majalisar Dattawa na hana Sanata Natasha yin magana yayin zaman majalisa na ranar 20 ga watan Fabrairu, 2025.
Wannan ya biyo bayan ƙin zama da ta yi a kujerar da aka ware mata.
Kotun ta jaddada cewa Shugaban Majalisar yana da ikon raba wa sanatoci wajen zama, kuma doka ta tanadi cewa sai sanata na zaune ne kawai yake da haƙƙin yin magana.
A ƙarshe, kotun ta kammala da cewa dukkanin matakan da majalisar ta ɗauka a kanta sun dace da doka, face batun tarar da ta soke.