Na Shekara Biyu Ina Kokarin Shawo Kan Mahaifina Ya Amince Da Shigata Kannywood —Iklima Umar Argungun
[ad_1]
Shafi ne da ya saba zakulo muku fitattun jarumai manya da kanana, daga cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood. Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wata Jarumar me shirin tasowa wato, IKLIMA UMAR ARGUNGUN Wacce aka fi sani da SUHAIRA ‘YAR AMANAR ADAMU ZANGO. Jarumar tayi batutuwa masu yawan gaske game da irin gwagwarmayar da ta sha a kokarin shigarta cikin masana’antar, tare da wasu kalubale da ta fuskanta bayan shigarta cikin masana’antar ta Kannywood. Dadin dadawa jarumar ta yi wani kira ga masu kokarin shiga cikin masana’kntar har ma da wasu batutuwan masu yawa.
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki
Sunana Iklima Umar Argungun, wacce aka fi sani da Suhaira ‘Yar Amanar Adamu Zango.
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Ni asalina babarbariya ce, mahaifiyata ‘yar Ghana ce, mahaifina yana zaune a birnin Kebbi karamar hukumar Argungun. Na yi makarantar firamare da Sakandire na a Sokoto, bayan an haife ni a Ghana kenan mun dawo Nijeriya. A yanzu ‘business’ kawai nake ban ci gaba da karatu ba, shekarata Ashirin da bakwai.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Abubuwa da yawa sun ja hankali na. Da farko dai tun a ‘primary school’ ina son dirama, in za a yi na kan yi aktin. Bayan tasowata na fara kallo sai na ji ina kaunar Adamu Zango, a takaice dai shi ya ja hankalina na shiga, shi da jarumarsa Nafisa Abdullahi.
Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?
Shekara takwas.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
Na sha gwagwarmaya ba kadan ba, musamman wajen mahaifina, na ci duka sosai kuma na nace. Saboda ni bana so na shiga harkar ba tare da izninsa ba, shi kuma yana yi wa fim wani irin kallon iskanci kawai ake yi a fim, ba zai yu ace ‘yar sa ta shiga fim ba. Balle muna da alaka da sarauta, na sha wahala wajen mahaifina sosai fa ba kadan ba. Mahaifiyata ce dai ba ni da damuwa da na kira ta sai ta saka min albarka. Saboda ita ma waka ta so Allah ne bai yi ba. Amma shi mahaifina sai da muka kusan shekara biyu muna abu daya da shi, da kyar dai na samu ya bar ni na shigo.
Da su wa kika fara haduwa a farkon shigarki kannywood?
Na hadu da mutane da yawa kamar su; Mama Adaman kamaye, Bashir Nayaya, Asma’u Sani, Lubabatu Madaki (Zinaru), Haj. Zulai Babejy, Baba Bashir Choroki, Sani Musa Danja, Yakubu Muhammad, da bestyna Maryam Abubakar, da su na fara haduwa.
Da wane fim ki ka fara?
Na fara da fim din ‘Dan Yau A Birni’, da Ado Gwanja. Lokacin shi ne wanda jama’a ke son gani ido rufe. ‘Scene’ daya nayi a fim din, amma wannan ‘scene’ dayan sai da ya janyo aka ta yi min magana saboda jarumin da muka yi aiki da shi, dakyar ma muka samu muka yi ‘scene’ din saboda bakin hanya ne, mutane sun yi dandazo.
Ya farkon farawar ta kasance?
Farko mun je ‘location’ ana ta jiran wata jaruma ta zo, a tunanina irin su Jamila Nagudu zan gani ko Fati Washa, ko Hadiza Gabon, ko Rahama Sadau. Har wajen sha biyu bata iso ba ana ta jaruma ake ta jira, can sai ga jarumar ta zo, wai ashe ‘besty’ na ake ta jira Maryam Abubakar (Rufaida Kwana Chasa’in). Wannan zaman ya bata min rai sosai, ni a tunanina bata kai a yi mata wannan jiran ba, a lokacin kenan. Amma gaskiya ban sha wata wahala ba.
Kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?
Ba laifi na dan yi finafinai, ba zan iya cewa ga yawansu ba.
Ko za ki iya fadowa masu karatu kadan daga sunayen finafinan da kika fito ciki?
Dajin dodo, DanYau A Birni, Tsakaninmu, kullaci, Sakayyar So, So Sone, Sadaki, Malamin So, Bora da Mowa, kadan daga ciki kenan.
Cikin fina-finan da ki ka fito wanne ne ya zamo bakandamiyyarki, wanda ki ka fi so, kuma me ya sa?
Kowane ina so amma na fi son Dajin Dodo, saboda na sha wahala. Kuma shi ‘dressing’ ne, ba ‘normal dressing’ ba. Kuma ni ‘yar sarauniyar Jeji ce, abubuwa dai na cikin Dajin Dodo na daban ne. Sannan ina son fim din So Sone.
Wane irin nasarori ki ka samu game da fim?
Na samu nasarori da dama game da fim, sanadiyyar fim na samu abubuwa da yawa. Na samu abin da ba kowa yake iya samunshi ba. Misali, akwai mutanen da akan Adamu Zango za su iya mutuwa ma, ko sati biyu da suka wuce da ya je Ghana wata tana ganinshi ta suma, amma ni ina daya daga cikin mutanen da za su daga waya su kira shi lokaci daya ya daga, ko bai daga ba zai biyo kira. Kin ga ko a nan na samu nasara sosai. Haka kuma dalilin fim idan na je gida Sokoto mutane za su yi ta kawon abinci da abubuwa daban-daban.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta cikin masana’antar Kannywood?
Gaskiya akwai kalubale da yawa, amma wanda ya fi tsaya min a rai shi ne, ka baro iyayenka a gida ka sha gwagwarmayar wajensu cewa za ka zo fim, kana ta kare harkar fim. Bayan ka zo kuma wanda kake saka ran zai yi maka fim din sai ya kawo nasa uzurin daban wanda baya ma kan tsari. Lokacin baka cikin abun, baka san yadda al’amuran suke ba, ka je ‘location’ tun safe ba a dora maka ‘camera’ ba, kuma ba a ce ba kai a cikin aiki ba, har dare yayi ba a baka na mashin ba, ba a san ya ka zo ba. Haka kuma za ka hakura dole ka kara komawa, washegari ka kara zuwa ‘still’ ba a dora maka ‘camera’ ba, wata ta kalle ki ma ta ce in kin yi, kin yi. In baki yi ba, baki yi ba.
Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farinciki ko akasin haka wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba a rayuwa?
Abun farinciki, saurayin da nake so a duniya ni na ganshi na ce ina son shi, sai ya kasance ma ya so ni fiye da yadda nake son shi. Ba hulakanci, ba tozarci, ina jin farincikin wannan. Na bakin ciki kuma, ina son na ga mama na kusa da ni, ta yi min nisan da ba damar na kwanta akan cinyarta, nayi kuka a kirjinta, na fada mata damuwar da yake damuna, tayi min nisan da kafin na je damuwar ya yi min illah. A kannywood kuma damuwar ita ce, na taba zuwa ‘location’ aka ajjiye ni kusan kwana hudu a jigawa, ashe ma ba ni da aiki. Kawai an tafi da ni ne, raina ya baci fiye da tunaninki. Na farinciki kuma Adamu Zango da na gani.
Hakan bai sa kin ji fim ya fita a ranki ba?
A’a wallahi, kullum kara ‘confidence’ nake akai, saboda ‘is my dream’.
Kafin shigarki masana’antar Kannywood bayan Adam Zango, wadanne jarumai ne suke burge ki, kuma me ya sa?
Adam A. zango, Nafisa Abdullahi, Rahama Sadau, Hadiza Gabon. Adamu kaunar sa nake, Nafisa tana kama da yayata Sahura, sauran kuma ‘acting’ dinsu ke burge ni.
Kin taba fim da Adamu Zango?
A’a! Ban taba fim da shi ba.
Ko kina da ubangida a masana’anyar Kannywood?
Kwarai ma kuwa, Hamadu dorayi baban Falalu dorayi.
Mene ne burinki na gaba game da fim?
Na zama jarumar da wasu za su yi kwaikwayona in saka dankwali wata ta yi irin daurin, ina so na zama ‘celebrity’ da duniya ba za ta taba mantawa da ni ba.
Yaushe za ki yi aure?
Kodayaushe ma wallahi a shirye nake, kawai ina jira Allah yayi ikon sa ne.
Kin taba yin saurayi a Kannywood?
Eh, na taba Akwai Mubarak wato Smart Aljalawi.
Wane kira za ki yi ga masu kokarin shiga Kannywood?
Wallahi kar su shigo, su yi zamansu. Su samu miji su yi aure, mu da muke ciki kuma Allah ya aurar da mu.
Me za ki ce da masoyanki masu kallon fina-finanki?
Ina matukar kaunarsu domin sune ni, idan ba su ba Suhairat. Kuma ina godiya sosai su ci gaba da sona, su kara akan wanda suke yi.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Ina gaishe da ke Rabi’atul Adawiyya, sai gaisuwata ga Hajiya Adaman Kamaye. Ubangiji ya kara kare ku.
Muna godiya, ki huta lafiya.
Ni na tafi.
[ad_2]
Source link