Gwamnatin Borno za ta soma bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye
[ad_1]
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da tura wa ƙananan hukumomin jihar 27 kuɗaɗensu kai tsaye kowane wata, kamar yadda doka ta tanada, zuwa asusunsu ba tare da tsaiko ba.
Muƙaddashin gwamnan jihar, Alhaji Dr. Umar Usman Kadafur, ne ya sanar da hakan yayin da yake jagorantar rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin 27 da aka zaɓa.
Kadafur ya ce matakin ya nuna jajircewar gwamnatin Gwamna Zulum wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya a matakin farko, tare da bin umarnin Kotun Ƙoli da kuma kiran da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa gwamnonin jihohi a watan Disambar 2025 kan bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin karɓar kuɗaɗensu kai tsaye.
A cewarsa, an ɗauki matakin ne domin ƙarfafa shugabannin ƙananan hukumomi ta hanyar ba su damar sarrafa kuɗaɗensu kai tsaye ba tare da katsalandan ba.
Muƙaddashin gwamnan ya ce: “Ya kamata ku kasance kusa da mutanenku. Kun san gwamnanmu mutum ne mai himma wajen ci gaban jiharmu.
“Muna sa ran ku kasance masu gaskiya da riƙon amana. Duk wata naira da kobo da kuka karɓa dole ne a yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace.
“Jihar Borno ce kaɗai a halin yanzu da ƙananan hukumominta ke karɓar rabon kuɗaɗensu kai tsaye zuwa asusunsu.”
Ya bayyana hakan a matsayin abin yabo ga hangen nesa da jajircewar Gwamna Zulum, yana mai cewa wannan mataki hujja ce cewa shugabanci na buƙatar haɗin gwiwa da gaskiya.
“Muna da yaƙini kan tsarin gudanar da ƙananan hukumomi, shi ya sa aka ba ku kuɗaɗenku kai tsaye domin ku yi aiki yadda ya kamata ga al’ummominku.
“Lokacin ƙorafi ya wuce. Ba za a sake bin diddigin gwamnati don neman sahalewar kashe kuɗaɗe ba,” in ji Kadafur.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da bayyana duk kuɗaɗen da ake bai wa ƙananan hukumomi domin tabbatar da gaskiya.
Muƙaddashin gwamnan ya kuma ɗora wa sabbin shugabannin ƙananan hukumomin alhakin kula da jin daɗin ma’aikatansu, tare da tabbatar da biyan albashi cikin gaggawa.
“Dole ne ku kula da kowace naira, ku gudanar da ayyuka bisa tsarin dabarunmu na shekaru 10, tare da mai da hankali kan abubuwan da ke inganta rayuwar al’umma kai tsaye,” in ji shi.
Ya kuma yi kira da a ba da muhimmanci ga tsaro, mutunci da ladabi a wuraren aiki, yana mai jaddada cewa dole ne dukkan ma’aikata su koma bakin aikinsu ba tare da wani uzuri ba.
Manyan baƙi da suka halarci taron rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin sun haɗa da Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Tahir Monguno; Sanata Kaka Shehu Lawan; Shugaban APC na Jihar Borno, Bello Ayuba; tsohon Mataimakin Gwamna, Ali Abubakar Jata’Au; Usman Mamman Durkwa, da sauran manyan jami’ai.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link