‘Za a yi duk mai yiwuwa domin kama makasan mutum 7 ’yan gida ɗaya a Kano’

[ad_1]



Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da kisan wata mata da ’ya’yanta shida a unguwar Ɗorayi Ciranci da ke birnin Kano, yana mai alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen kamo waɗanda suka aikata wannan ta’asa domin gurfanar da su gaban doka.

Gwamnan ya bayyana kisan a matsayin rashin imani da kuma mummunan cin zarafin bil’adama, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya shafa, mazauna unguwar, da kuma ɗaukacin al’ummar Jihar Kano.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda ya jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunci aikata irin wannan ta’addanci ba.

Aminiya ta ruwaito cewa wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kutsa gidan wani mazaunin unguwar, Haruna Bashir, inda suka kashe mai ɗakinsa da yaransa guda shida, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da ɗimuwa.

Waɗanda aka kashe sun haɗa da Fatima Abubakar mai shekaru 35, da ’ya’yanta: Maimuna (’yar shekara 17), Aisha (16), Bashir (13), Abubakar (10), Faruk (7), da Abdussalam, wanda bai wuce shekara ɗaya da rabi ba.

Bayanai sun ce maharan sun yi amfani da muggan makamai wajen aiwatar da kisan.

A nasa ɓangaren, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa tuni Kwamishinan ’yan sanda Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano masu hannu a kisan.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *