Sin Za Ta Aiwatar Da Matakan Bunkasa Sayayya Da Bude Kofa A Shekarar 2026
[ad_1]
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin za ta aiwatar da matakan bunkasa sayayya, da bude kofa, a wani bangare na muhimman ayyukan da za ta gudanar a shekarar nan ta 2026. An bayyana hakan ne a yau Lahadi, gabanin rufe taron yini biyu da aka shirya dangane da ayyukan cinikayya.
Yayin taron, an bayyana yadda tsarin ayyukan cinikayya na kasar zai ingiza gudanar da matakan zaburar da sayayya, da gina sha’awar sayen kayayyaki masu tamburan cikin gida, ta hanyar yaukaka sabbin alkaluman ci gaba a fannin hada-hadar samar da hidimomi, da kyautata manufofin sayayyar kaya ta musayar tsaffin kayayyaki da sababbi.
Bugu da kari, taron ya jaddada batun sayayya a fagen hajojin dijital, da marasa dumama yanayi, da masu nasaba da kiwon lafiya, da hajojin dake fitowa daga sabbin sana’o’i daga dukkanin sassan kasar ta Sin.
Domin fadada bude kofa kuwa, Sin za ta daidaita ka’idojin raya cinikayyar kasa da kasa masu matukar inganci, da daga matsayin yankunan gwaji na cinikayya cikin ‘yanci, da yankin gudanar da cinikayya marar shinge na gabar teku dake Hainan, da karbar bakuncin muhimman tarukan nune-nunen hajoji yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link