“Dalilin da ya sa za mu saki mutum 70 da ake zargi da ta’addaci a Katsina”
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana dalilin da ya sa take shirin sakin mutum 70 da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi ta’addanci.
Gwamnatin ta ce matakin yana daga cikin yarjejeniyar zaman lafiya da ta ƙulla da masu ɗauke da makamai a jihar.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida na jihar, Nasir Mu’azu, ya ce sakin mutanen zai taimaka wajen ƙarfafa yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin al’ummomin da abin ya shafa da kuma ’yan bindiga da suka ajiye makamai.
Mu’azu, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da DCL Hausa a ranar Asabar, bayan da jama’a suka nuna fushinsu kan wata wasiƙa da ta nuna cewa gwamnatin jihar ta nemi kotu ta taimaka wajen sakin mutanen da ake tuhuma.
A cewarsa, yarjejeniyar zaman lafiyar ta shafi ƙananan hukumomi 15, kuma ta taimaka wajen ceto kusan mutum 1,000 da ’yan bindiga suka sace.
Ya kwatanta matakin da abin da ke faruwa a lokacin yaƙi, inda ɓangarorin da ke faɗa da juna ke musayar fursunoni.
Wasiƙar da ta janyo ce-ce-ku-ce
Taƙaddamar ta fara ne bayan wata wasiƙa mai ɗauke da tambarin “SIRRI” mai kwanan wata 2 ga watan Janairu ta bayyana a kafafen sada zumunta.
Jaridar Sahara Reporters ce ya fara wallafa wasiƙar wadda ta nuna shirin da gwamnatin ke yi na sakin waɗanda ake tuhumar.
Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Katsina ce ta rubuta wasiƙar, inda ta aike ta zuwa ga Babban Alƙalin jihar.
Wasiƙar ta nemi sanya hannun Kwamitin Bibiyar Aiwatar da Dokar Shari’a da Laifuka (ACJMC), domin taimakawa wajen sakin mutanen.
Daraktan Ƙara na jihar, Abdur-Rahman Umar ne, ya sanya hannu a kan wasiƙar.
Wasiƙar ta bayyana cewa an tura sunayen mutum 48 da ake zargi da laifukan harkar ’yan bindiga daga Ma’aikatar Tsaro zuwa Ma’aikatar Shari’a.
Ma’aikatar ta ce sakin mutanen na daga cikin sharuɗan ci gaba da yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla tsakanin wasu ƙananan hukumomi da ’yan bindiga.
Wasiƙar ta ƙara da cewa, wasu daga cikin mutanen an riga an gurfanar da su a gaban kotu, yayin da sauran ke tsare suna jiran shari’a a kotunan majistare daban-daban a faɗin jihar.
Haka kuma, an tura wasu sunayen fursunoni 22 da ke fuskantar shari’a a manyan kotuna domin a duba yiwuwar sakin su sakamakon yarjejeniyar zaman lafiyar.
Martanin Jama’a
Bayan bayyanar wasiƙar, ’yan Najeriya da dama ciki har da lauyoyi da ƙungiyoyi masu zaman kansu sun soki shirin.
Sun ce sakin mutanen da ake zargi da manyan laifuka na iya raunana dokar ƙasa, hana waɗanda aka cutar samun adalci, da kuma taimaka wa wajen sake aikata laifuka.
Martanin Gwamnati
Da yake mayar da martani, Nasir Mu’azu ya ce yarjejeniyar zaman lafiyar ta haifar da sakamako mai kyau, musamman wajen kuɓutar da mutanen da aka sace.
Ya bayyana adadin mutanen da aka kuɓutar daga wasu ƙananan hukumomi, ciki har da Sabuwa (310), Bakori (125), Danmusa (60), Dutsinma (62), da Safana (36).
Ya ce a ko ina a duniya, idan an kammala yaƙi, ana yin musayar fursunoni.
Ya kawo misali da yaƙin basasar Najeriya da kuma tattaunawar da aka taɓa yi da Boko Haram.
A cewarsa, babban abin da ake nema shi ne samar da zaman lafiya, ba wai hukunta masu laifi ba kawai.
Mu’azu, ya jaddada cewa matakan da Ma’aikatar Shari’a da kotuna suka ɗauka ba su saɓa wa doka ba.
Ya ƙara da cewa duk wanda bai gamsu da matakin ba na iya garzaya wa kotu domin neman haƙƙinsa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link