Yajin Aiki: Duk Wanda Ya Ƙi Komawa Aiki Bayan Umarnin Kotu Zai Fuskanci Hukunci – Wike
[ad_1]
Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya gargaɗi ma’aikatan Abuja da ke yajin aiki da cewa duk wanda ya ƙi komawa bakin aiki daga ranar Laraba, 28 ga watan Janairu, bayan umarnin kotu, zai fuskanci hukunci.
Wike ya faɗi hakan ne a ranar Talata yayin ganawarsa da manema labarai a ofishinsa da ke Abuja, jim kaɗan bayan kotu ta umarci ma’aikatan da su dakatar da yajin aikin.
- Tsaro: Sojoji Sun Gano Masana’antar Ƙera Makamai A Nasarawa
- Gwamnatin Turkiyya Na Shirin Zuba Jarin Kasuwanci Na Dala Biliyan 5 A Nijeriya — Shugaba Erdogan
“Daga gobe duk wanda bai koma aiki ba, za mu ɗauki mataki a kansa. Idan muka ga wani yana ƙoƙarin hana wasu zuwa aiki, za mu hukunta shi. Dole ne doka ta yi aiki,” in ji Wike.
Ministan ya ce gwamnati ta riga ta gana da ƙungiyoyin ƙwadago kuma an tattauna ƙorafe-ƙorafensu, amma ba a cimma matsaya ba.
“Idan ma’aikata sun kawo buƙatu 14, gwamnati ta warware 10 daga ciki, to me kuma suke so?” ya tambaya.
Ma’aikatan sun tsunduma yajin aiki ne tun a makon da ya gabata, suna neman a inganta yanayin aikinsu da alawus-alawus ɗinsu.
Yajin aikin ya jawo rufe ofisoshi da dama na gwamnati a Abuja, lamarin da ya hana jama’a yin wasu muhimman ayyuka.
Biyo bayan haka ne Wike ya kai ƙara kotu, wacce ta umarci ma’aikatan da su dakatar da yajin aikin.
[ad_2]
Source link