Xi Ya Bukaci A Karfafa Nazari Daga Tushe Don Inganta Aikin Kirkire-Kirkire
[ad_1]
Kwanan baya, babban sakataren kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, shugaban kasa, kana, shugaban kwamitin tsakiya na soja, Xi Jinping ya ba da umurni game da aikin kwamitin asusun kimiyya da fasahar halitta na kasar Sin wato NSFC. Ya ce, cikin shekaru 40 da suka gabata, wato tun bayan kafa NSFC zuwa yanzu, kwamitin ya taka muhimmiyar rawa kan ayyukan inganta nazari daga tushe, da horar da masana, da dai sauransu.
Haka kuma, Xi Jinping ya jaddada fatan ganin kwamitin ya yi amfani da damammakin da ake samu na yin kwaskwarimar kimiyya da fasaha da masana’antu, domin karfafa tsarin nazari daga tushe bisa manyan tsare-tsare, da idon basira. Kana, a zurfafa aikin yin kwaskwarimar Asusun kimiyya da fasaha, domin kyautata tsarin samar da tallafin kudi, da inganta aikin samar da tallafi ga ayyukan nazari, ta yadda za a shimfida yanayi mai kyau na nazarin kimiyya da fasaha, tare da habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa. A sa’i daya kuma, ya bukaci a karfafa wa masu aikin kimiyya da fasaha gwiwar neman ci gaba, tare da fitar da muhimman sakamakon yin kirkire-kirkire da kansu, ta yadda za su ba da karin gudummawa wajen raya kimiyya da fasaha, da gina kasa mai ci gaba a fannin kimiyya da fasaha.
A watan Fabrairun shekarar 1986, aka kafa kwamitin asusun kimiyya da fasahar halitta na kasar Sin wato NSFC, zuwa yanzu, kwamitin ya zama wata muhimmiyar kafar samar da tallafin kudi ga masu nazarin kimiyya da fasaha ta fuskar yin nazari daga tushe. (Mai Fassara: Maryam Yang)
[ad_2]
Source link