MDD ta sanya Najeriya cikin ƙasashe 16 da ke fama da tsananin yunwa
[ad_1]
Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP), ta ayyana Najeriya ɗaya daga cikin jerin ƙasashen da za su fuskanci matsananciyar yunwa.
Ta kuma yi gargaɗin cewa ƙarin mutane a duniya na iya fuskantar yunwa saboda ƙarancin kuɗin tallafi.
Rahoton da Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) da WFP suka fitar, ya nuna cewa rikice-rikice da tashin hankali ne ke jawo matsananciyar yunwa a ƙasashen da ke cikin hatsari.
Rahoton ya bayyana ƙasashen Haiti, Mali, Falasdinu, Sudan ta Kudu, Sudan da Yemen a matsayin waɗanda ke cikin mafi munin hali inda jama’a ke fuskantar barazanar yunwa mai tsanani.
Haka kuma, Afghanistan, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Myanmar, Najeriya, Somaliya da Siriya sun shiga jerin ƙasashe masu matuƙar damuwa.
Rahoton ya kuma ambaci Burkina Faso, Chadi, Kenya da kuma yanayin ’yan gudun hijirar Rohingya a Bangladesh.
Darakta Janar na WFP, Cindy McCain, ta ce, “Muna fuskantar matsalar yunwa da za a iya kauce mata gaba ɗaya, amma idan ba a ɗauki mataki ba, hakan zai haifar da ƙarin rikici da rashin kwanciyar hankali.”
Rahoton, ya ce kuɗin agajin jin-ƙai yana raguwa sosai, inda aka samu dala biliyan 10.5 kacal daga cikin dala biliyan 29 da ake buƙata don taimaka wa waɗanda ke cikin hatsari.
Saboda ƙarancin kuɗi, WFP ta rage tallafa wa ’yan gudun hijira da waɗanda aka raba da muhallinsu, sannan ta dakatar da shirye-shiryen ciyar da ɗalibai a wasu ƙasashe.
Hukumar FAO kuma ta yi gargaɗin cewa harkar noma na cikin hatsari, wanda shi ne ginshiƙin samar da abinci da hana matsalolin yunwa sake faruwa.
An bayyana cewa tallafi ake buƙata don samar da iri da kula da dabbobi kafin lokacin shuka ko wani sabon rikici ya sake ɓarkewa.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link