Babban Sakataren AL Ahmed Aboul Gheit: An Sada Zumunta Mai Zurfi Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa
[ad_1]
A yayin aka cika shekaru 70 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, babban sakataren kungiyar AL Ahmed Aboul Gheit ya yi hira da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, inda ya bayyana cewa, sau da dama ya kawo ziyara kasar Sin, ya ga yadda Sin ta samu ci gaba cikin sauri.
Gheit ya bayyana cewa, ci gaban kasar Sin ya burge duniya sosai, dalilin da ya sa hakan shi ne gudummawar da shugabannin kasar Sin da kuma jama’arta suka samar tare, ya ce, an sada zumunta a tsakanin Sin da kasashen Larabawa mai zurfi da samun kyakkyawar makoma.
Ban da wannan kuma, Gheit ya yi nuni da cewa, kasar Sin ba ta tsoma baki kan harkokin cikin gida na sauran kasashe, kana ba ta gabatar da bukatarta daga bangare daya yayin da take yin hadin gwiwa tare da sauran kasashe, Sin ta sada zumunta da yin hadin gwiwa cikin adalci tare da kasa da kasa. Gheit yana fatan bangarorin biyu za su samu bunkasa mai dorewa yayin da suke yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da siyasa. (Zainab Zhang)
[ad_2]
Source link