2027: Tinubu Na Son A Naɗa Shi Sarauta Ne, Ba Zaɓe Ba — Dino Melaye

[ad_1]

Tsohon Sanata mai wakiltar Yankin Kogi ta Yamma a Jihar Kogi, kuma jigo a jam’iyyar ADC, Dino Melaye, ya yi zargin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ya sha’awar a fafata ta dimokuraɗiyya a zaɓen shekarar 2027, sai dai yana neman abin da ya kira “naɗa shi sarauta” a matsayin Shugaba.

Haka kuma, ya yi zargin cewa, jam’iyyar mai mulki ta APC ta ƙara shiga ruɗani sakamakon ƙaruwa da tasirin jam’iyyar haɗin gwiwar ‘yan adawa, wato ADC.

  • Yadda Jigo A APC Na Kano Ya Rasu A Otal A Abuja
  • Zulum Ya Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 150 Ga Iyalan Jami’an Soji Da Suka Rasu.

Melaye ya bayyana hakan ne a shirin ‘Breakfast show’ na gidan talabijin na ‘Channels’ a ranar Alhamis, inda ya yi zargin cewa damuwar da jam’iyyar mai mulki ke nunawa game da ADC ba kawai gasa ta siyasa ba ce, illa wani babban barazana ga ƙa’idojin dimokuraɗiyya a ƙasar.

Melaye ya ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ba ya nuna sha’awar fafatawa ta dimokuraɗiyya, sai dai yana neman tsarin siyasa da zai ba shi damar riƙe Shugabanci ta kowane hali.

Ya ce: “Bola Ahmed Tinubu yana son a naɗa shi sarauta ne; ba ya son a yi zaɓe.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *