An kashe mutum 2, wasu sun jikkata a sabon hari a Filato

[ad_1]



’Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari a unguwar Ban da ke maƙwabtaka da Kwalejin Fasaha ta Jihar Filato, inda suka hallaka mutum biyu tare da jikkata wasu da dama.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun farmaki yankin ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Laraba, inda suka buɗe wuta babu ƙaƙƙautawa.

Aƙalla mutum uku ne suka tsallake rijiya da baya da raunukan harbin bindiga, waɗanda a halin a yanzu suke karɓar magani a asibiti.

Hari. ya jefa ɗalibai da ke zaune a wajen makarantar cikin fargaba.

Wata ɗaliba mai suna Nanchip Dube, ta bayyana cewa ƙarar harbin ta jefa mazauna yankin cikin ruɗani da tashin hankali.

A wani lamari makamancin wannan da ya faru a Ƙaramar Hukumar Riyom, ’yan bindiga sun yi wa wasu matasa kwanton-ɓauna a kan hanyar ƙauyen Baten zuwa Du’a da misalin ƙarfe 8:15 na dare.

Wannan harin ya yi sanadiyar ajalin wani matashi mai shekaru 27, Amos Monday, wanda ɗan asalin kauyen Du’a ne.

Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar matasan Berom (BYM), Rwang Tengwong, ya tabbatar wa manema labarai aukuwar waɗannan hare-hare a Jos.

Ya yi kira ga mazauna yankunan Kwi, Wereng da sauran maƙwabtan Ƙananan Hukumomin Jos ta Kudu, Barkin Ladi da kuma Riyom da su ƙara ƙaimi wajen sanya idanu kan harkar tsaro.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Filato, SP Alfred Alabo, ya faskara, domin bai amsa sakon kar-ta-kwana da aka aike masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *