Bayan biyan N50m ma’aurata da ’yarsu su da aka yi garkuwa da su a Katsina

[ad_1]



Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina.

Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da su a kan naira miliyan 50.

Mahaifin Halimatu, Alhaji Ali Turare, ya tabbatar da biyan kuɗin kafin a sako ’yarsa da mijinta da jikarsa.

“Bayan kwana uku da biyan kuɗin ne suka kira mu ta waya, suka ce an sako su, a je a karɓe su a Gurbin Ɓaure. Yanzu haka duk suna asibiti ana duba lafiyarsu,” in ji shi.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wani bayani da ya fito daga bakin rundunar ’yan sandan jihar Katsina game da lamarin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *