He Lifeng Zai Halarci Taron Dandalin Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Na Duniya Na Bana Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Switzerland
[ad_1]
Memba a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana mataimakin firaministan kasar Sin, He Lifeng, zai halarci taron dandalin tattauna batutuwan tattalin arziki na duniya na shekarar nan ta 2026, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar Switzerland.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana hakan a Jumma’ar nan, yana mai cewa He zai halarci taron dandalin na birnin Davos da ziyartar kasar Switzerland bisa gayyatar da ya samu daga dandalin gami da gwamnatin Switzerland, tsakanin ranakun 19 zuwa 22 ga watan nan na Janairu. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link