Sin Ta Samu Kyautatuwar Muhallin Halittu A Shekarar 2025
[ad_1]
Wasu bayanai da aka fitar yayin taron nazarin aikin kare muhallin halittu na kasar Sin na shekarar nan ta 2026, sun nuna yadda kasar ta samu kyautatuwar muhallin halittu a shekarar 2025 da ta gabata, sakamakon aiki tukuru da aka yi a fannin yaki da gurbatar muhalli, da wanzar da manufar samun ci gaba ba tare da lalata muhalli ba.
Taron ya kuma bayyana cewa, matsakaicin tasirin gurbatar muhalli kan mizanin PM2.5 a shekarar ta da gabata, ya tsaya ne kan micrograms 28 kan duk kyubik mita, adadin da ya ragu da kaso 4.4 bisa dari a mizanin shekara-shekara.
Kazalika, adadin ranakun da aka samu tsaftatacciyar iska ya karu da maki kaso 1.9 bisa dari, zuwa kaso 89.3 bisa dari a shekarar ta 2025, yayin da mizanin tsaftar ruwa a gabar tekun kasar ya karu zuwa kaso 84.9 bisa dari, karuwar da ta kai ta maki kaso 1.2 bisa dari.
Ma’aikatar kare muhallin halittu da muhalli ta kasar Sin, ta ayyana muhimman ayyukan da za ta gudanar a shekarar nan ta 2026, ciki har da bunkasa kandagarkin gurbacewar muhalli, da karfafa lura da yanayin muhalli da gaggauta kirkire-kirkiren fasahohi. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link