Ana cece-kuce kan yunƙurin Amurka na haramta Shari’ar Musulunci a Najeriya

[ad_1]



Ɓangaren doka na Gwamnatin Amurka, ya buƙaci a tilasta wa Najeriya daina amfani da shari’ar musulunci gaba ɗaya, a wani yunƙuri na ganin an daina abin da suka kira “muzguna wa kiristoci” a ƙasar.

Majalisar Wakilan Amurka ce bayar da wannan shawara bayan ta kammala tare da miƙa rahoton binciken da ta yi kan zargin muzgunawa da kashe Kiristoci a Najeriya, lamarin da ya daɗe yana jan hankali tare da haifar da zazzafar muhawara.

Ɗan Majalisar Wakilan Amurka, Riley M. Moore ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, wadda ya bayyana a matsayin rahoton da za su miƙa wa Shugaban Amurka Donald Trump.

Moore ya ce rahoton ya ƙunshi cikakken bayanin kan abin da suka bankaɗo da kuma wasu matakan da suke so a ɗauka domin “kawo ƙarshen muzgunawa Kiristoci a Najeriya.”

Sauran ’yan majalisar da suka taya Moore aikin sun haɗa da wasu ’yan kwamitin majalisar kan kasafin kuɗi da na harkokin ƙasashen waje, waɗanda suka garzaya uwa fadar gwamnatin Amurka domin miƙa rahoton a hukumance.

Sun yi wannan aikin ne bayan an kafa kwamitin bincike a majalisa, biyo bayan ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ke buƙatar sa ido da Trump ya yi a ranar 31 ga watan Oktoban 2025.

Tun a lokacin ne Trump ya buƙaci Moore da shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar Amurka, Tom Cole, da su jagoranci wani kwamiti na musamman domin gano gaskiyar zargin muzguna wa Kiristoci da sauran matsalolin tsaro a Najeriya.

Ya ce, “wannan rahoton ya biyo bayan nazari da bincike na watanni, ciki har da zuwa da ’yan majalisar Amurka ta yi Najeriya domin bincike da tattaunawa da masana da jagororin addini da ma tattaunawa da ’yan gudun hijira da kuma manyan jami’an gwamnatin Najeriya,” in ji Moore.

A sanarwar da Moore ya fitar bayan miƙa rahoton binciken, ya ce sun ba gwamnatin Amurka wasu muhimman shawarwari na matakan da suke so a ɗauka domin magance matsalar.

Manyan shawarwarin da suke ƙunshe a cikin rahoton

Shiga yarjejeniyar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya domin kare garuruwan Kiristoci da ke fuskantar muzgunawa da fatattakar mayaƙa masu iƙirarin jihadi.

Dakatar da wasu tallafi da ake bai wa Najeriya har sai an ga matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka wajen hana muzguna wa Kiristoci.

Sanya takunkumi da hana biza ga ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da suke da hannu a tauye ’yancin gudanar da addini.

Taimakon gwamnatin Najeriya domin daƙile ayyukan Fulani masu riƙe da makami, ciki har da daina fitar da shanu da namansu zuwa wasu ƙasashe maƙwabta.

Neman soke shari’ar Musulunci da kisa kan ɓatanci a Najeriya.

Taƙaita hulɗa da Rasha da China da buƙatar a riƙa aiki tare da ƙasashen waje irin su Faransa da Hungary da Birtaniya domin samun nasara,

Malaman addini sun soki rahoton

Wasu shugabannin addinin Islama a Najeriya ciki har da Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, Babban Sakataren Jama’atul Nasrul Islam JNI, sun yi kakkausar suka kan rahoton da ’yan majalisar Amurka suka gabatar wa Trump.

Ita ma dai a nata ɓangaren, Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN, ta yi gargaɗi game da kiran ’yan majalisar Amurkan suka yi na soke tsarin shari’ar Musulunci da kuma dokar ɓatanci ga fiyayyen halitta a Najeriya, wanda ta ce hakan zai iya ƙara rura wutar rikicin addini a ƙasar.

CAN ta ce maimakon soke dokar shari’ar Musulunci a Najeriya, kamata ya yi a samar da wani sabon kudin tsarin mulki, wanda zai yi adalci ga kowane addini da kuma ƙabila a ƙasar.

Fitaccen malamin addini na Kaduna, Ahmad Gumi, ya kare matakin aiwatar da Shari’a, yana cewa Musulmi na da ‘yancin a yi musu hukunci da dokokin addininsu kamar yadda wasu ƙasashe ke kare nasu manufofi.

Ya ce ba Musulmi kaɗai ba ne ke fama da hare-hare, yana mai zargin akwai wasu ɓoyayyun al’amura da ke rura wutar rikici a ƙasar.

Shi ma Sheikh Halliru Maraya ya shaida cewa matsalar tsaro a Najeriya babu wani addini guda da ƙyale.

“Da Musulmi da Kirista duk ana kashewa,” in ji shi, yana mai gargaɗin cewa duk wani mataki daga ƙetare ya kamata ya mutunta ikon Najeriya a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.

Ana so a tsokano tsuliyar dodo — Hakeem Baba Ahmed

Tsohon mai magana da yawun Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana rahoton ’yan majalisar Amurkan a matsayin wani da ya yi kama da tsokano tsuliyar dodo.

Dattijon ya bayyana cewa kawo batun soke shari’ar musulunci na nufin buɗe wata muhawara da kundin tsarin mulki ya riga ya warware, inda ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya tashi tsaye domin kare martabar ƙasar nan.

‘Har yanzu Amurka ba ta fahimci matsalar tsaron Najeriya ba’

A ɓangaren masana, Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce har yanzu Amurka ba ta fahimci lamarin ba domin kuwa tana kallon matsalar tsaron Najeriya da ido ɗaya, alhali rikici ne mai matuƙar sarƙaƙiya da ya kamata a tsaya a yi masa karatun ta nutsu.

Kazalika, Farfesan ya jaddada cewa ba hurumin wata ƙasa ba ce ta tsara wa Najeriya manufofin tsaronta.

Tsohon jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Ambasada Ibrahim Kawu, ya kuma ce wajibi ne Najeriya ta tsaya tsayin daka wajen kare ikon ta a harkokin cikin gida.

Martanin Gwamnatin Najeriya

A martaninta, Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ta ce rahoton zai iya zama wata dama ta faɗaɗa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, amma cikin mutunta tsarin mulkin Nijeriya da ikon ta.

Ya jaddada cewa Nijeriya ba ta da manufar tsananta wa wani addini, kuma kundin tsarin mulkin ƙasar ya tabbatar da ‘yancin addini ga kowa.

Ya ce gwamnati na ci gaba da ƙarfafa ayyukan soji da na jami’an tsaro domin murƙushe ta’addanci, fashi da makami da rikice-rikicen ƙabilanci da suka addabi sassan ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *