Gwamnatin Tarayya Ta Ce Ba Ta Taɓa Goyon Bayan Musguna Wa Kiristoci Ba

[ad_1]

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba ta taɓa goyon bayan musguna wa Kiristoci ko nuna wariyar addini ba, bayan da Majalisar Wakilan Amurka ta fitar da rahoto kan zargin cin zarafin Kiristoci a Nijeriya.

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ce matsalolin da ake samu a wasu yankuna ba na wariya ba ne, amma sun samo asali ne daga ta’addanci, fashi da makami, da rikice-rikicen al’umma.

  • ‘Yan Majalisar Dokokin Adamawa 6 Sun Fice Daga Jami’yyar PDP
  • Gwamnatin Jigawa Na Ƙoƙarin Ganin DSS Ta Saki Walida — Umar Namadi

Ya ce tsarin mulki yana bai wa kowane ɗan Nijeriya ‘yancin addini da ibada, kuma gwamnati na nan daram wajen kare wannan ‘yanci da tabbatar da adalci ga kowa.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnati na ƙarfafa haɗin gwiwar jami’an tsaro a wuraren da matsala ta ke, tare da yaƙi da ta’addanci da masu garkuwa da mutane, da kama manyan masu laifi.

Haka kuma, gwamnatin ta inganta haɗin gwiwa da hukumomi don saurin ɗaukar mataki, musamman a yankunan karkara masu rauni.

Sanarwar ta jaddada muhimmancin dangantaka tsakanin Nijeriya da Amurka, tana mai cewa ƙasar na maraba da tattaunawa da haɗin kai bisa mutunta juna.

Rahoton Majalisar Wakilan Amurka kan zargin cin zarafin Kiristoci an gabatar da shi ga shugaban Amurka Donald Trump a ranar Talata.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *