’Yan sanda sun kama gungun masu fashi a kan hanyar Katsina zuwa Kano

[ad_1]



Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama gungun mutane 11 da ake zargi da kasancewa ’yan fashi da makami da ke addabar matafiya a kan hanyar Katsina zuwa Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abubakar Aliyu, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba a Katsina cewa waɗanda ake zargin sun kware wajen tare hanyoyin zuwa Sha’iskawa-Charanchi da Katsina-Kankia-Kano, suna kwace dukiyoyin matafiya.

Ya bayyana sunayen waɗanda aka kama da suka haɗa da Dikko Ma’aru, Dardau Kabir, Muntari Musa, Labaran Amadu, Usman Ma’aru, Lawal Zubairu, Nasiru Sanusi, da Adamu Kabir.

Sauran sun haɗa da Abdullahi Zubairu, Muhammad Usman da Sale Shehu, dukkaninsu ’yan tsakanin shekaru 21 zuwa 35.

Ya ce, “Nasarar ta samu ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10 na safe lokacin da aka cafke ɗaya daga cikin gungun yayin da yake ƙoƙarin sayar da wasu kayayyakin da suka yi fashin su, bayan samun sahihin bayanan sirri.

“Bayan samun wannan bayani, jami’anmu sun bi sahu suka kama wanda ake zargin, lamarin da ya kai ga kama sauran ’yan gungun,” in ji shi.

Kakakin ’yan sandan ya ce yayin bincike, an samu agogo guda 80, wayoyi 9 da wuka daga hannun waɗanda ake zargin a matsayin shaidu.

Ya ƙara da cewa Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Bello Shehu, ya yaba da ƙoƙarin jami’an da suka gudanar da aikin, tare da nuna godiya ga goyon bayan jama’a.

Aliyu ya rawaito Kwamishinan yana ƙara kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da muhimman bayanai da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka a jihar.

Ya kuma ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *