Jami’ar Gwamnatin Tarayya Da Ke Gusau Ta Yi Sabon Shugaba, Farfesa Tukur Adamu
[ad_1]
Sabon Mataimakin Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau ( FUGUS) Farfesa Tukur Adamu ya kama aiki a matsayin maitaimakin shugaban Jami’ar (VC).
Farfesa Tukur Adamu, shi ne mataimakin Shugaban Jami’a na huɗu da ya karɓi ragamar mulki daga mataimakin shugaban Jami’ar Farfesa Mu’az Abubakar Gusau mai barin gado.
- Shekaru 55 Da Kulla Diflomasiyya: Akwai Kyakkawar Huldar Abota Tsakanin Sin Da Najeriya
- An Gudanar Da Bukukuwa Iri-Iri Don Maraba Da Zuwan Bikin Bazara Na Sin A Kasashe Da Dama
Farfesa Mu’az Abubakar Gusau ya jagoranci Jami’ar daga shekara ta 2021 zuwa 2026 a matsayin mataimakin shugaban Jami’ar na uku.
Da yake jawabi a lokacin miƙa mulki, mataimakin Shugaban Jami’ar mai barin gado, Farfesa Gusau ya gode wa shugabannin Jami’ar, da masu ruwa da tsaki da kuma al’ummar Jami’ar bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake riƙe da mukamin mataimakin shugaban Jami’ar.
Farfesa Gusau, ya buƙaci sabon mataimakin shugaban Jami’ar da ya ci gaba da bunkasa Jami’ar a fannin koyarwa, bincike da kuma ilmantarwa.
Da yake jawabi a yayin taron, sabon mataimakin shugaban, ya yi alkawarin yin aiki tare da shugabanni, al’ummar da ke makwabtaka da Jami’ar da dukkan masu ruwa da tsaki don bunkasa Jami’ar”.
Farfesa Adamu ya yi kira ga shugabannin jami’ar da masu ruwa da tsaki da kuma al’ummar Jami’ar da su ba shi goyon baya da yake bukata don bunkasa Jami’ar
[ad_2]
Source link