Ina Fatan Zama Ɗaya Daga Cikin Manyan Mawaƙa A Afirka – Aminu Kabuga

[ad_1]

Shafi ne da ya saba zaƙulo muku fitattun Jarumai da mawaƙa manya da ƙanana har ma da masu ƙoƙarin tasowa, daga cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood. Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wani fasihin mawaƙi kuma jarumi a cikin masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood wato, AMINU ƊAHIRU ABDULLAHI wanda aka fi sani da AMINU KURDAN KABUGA. Inda ya bayyanawa masu karatu irin gwagwarmayar da ya sha domin haɗuwa da mawaƙin da ya fi so, tare da irin nasarorin da ya samu sanadiyyar waƙa, har ma da wasu batutuwan masu yawa.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanka tare da sunan da aka fi saninka da shi.

Sunana Aminu Ɗahiru Abdullahi wanda aka fi sani da Aminu kurɗan Kabuga.

Ko za ka faɗawa masu karatu ɗan taƙaitaccen tarihinka?

An haife ni a unguwar Kabuga layin firamare, inda nayi karatun firamare a ‘Bin Mas’ud Ƴan Azara’. Nayi Jss Kabuga, SS Ɗorayi babba, nayi NCE a FCE Kano, yanzu kuma ina ‘Leɓel 1, FUDMA UNIƁERSITY CSC Department’.

  • Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba
  • An Samu Manyan Nasarori A Kannywood A ‘Yan Shekarun Nan –Maryan CTB

Me ya ja hankalinka ka tsunduma harkar waƙa?

Dalilin mawaki Ado Gwanja, lokacin bikin ƙanin mahaifina Baba Raji. Ranar ana ta cewa Ado Gwanja zai zo mata suna ta kurantawa, ni ma nace sai na je na ganshi, muka je Ado ya zo yayi waƙa sai na ji abun ya burge ni ni ma ina so, tun daga lokacin na zama masoyin Ado Gwanja ni ma na fara rubutun waƙa. Haka na tara su har naso na kai masa domin ya duba min ko na yi daidai, haka na yi ta yin sunturin zuwa studio ɗin sa amma ban taɓa samun ganin sa ba.

Sai na haƙura na bi hanyar tura saƙo mafi sauƙi wato ‘Waƙa’ nayi masa, duk da haka ban sami ganinsa ba. Lokacin da na je yin waƙar da na ɗora muryar sai suka ji kamar Ado Gwanjan, sai aka yi ta bani shawarar na cigaba da waƙar saboda muryar. A hankali ina ta yi har mutane suka yi ta nemana zan musu waƙar bikinsu, kuma ni ma na ɗauki ɓangaran layin waƙar mata wajan biki, a haka nake har yanzu. Alhamdulillah

Za ka yi kamar shekara nawa da fara waƙa?

Na kai shekara bakwai.

Bayan waƙa kana yin fim ne?

Ina yin waƙa, ina yin fim.

Ya batun iyaye lokacin da ka sanar musu kana son fara waƙa, shin ka samu wani ƙalubale daga gare su ko kuwa?

Mahaifiyata ta san ina da sha’awar waƙar, amma har na fara ban faɗa musu ba, kuma ko da suka ji fatan alkhairi suka yi min. Muna zaune lafiya har ina fita wasu garuruwan nayi waƙa na dawo lafiya.

Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?

To, ni dai babu wanda ya koya min rubutun waƙa, wajan ɗorawa kuma akwai Alphazazi Muhammad shi ne wanda yayi min ƙoƙari sosai.

Idan na fahimce ka, kana so ka ce da kanka ka fara rubuta waƙa ba tare da wani ya koya maka ko ya ɗora ka akan hanya ba, ko kuwa ya kake nufi?

Babu wanda ya koya min rubutun waƙa da kaina nake komai, a studio ne wajan ɗora kiɗa Yusuf da yayansa Idris 1 Boy Nagudu da Alphazazi Muhammad Kabuga, suka taimaka min.

Da wacce waƙa ka fara?

Ita ce wacce na yi wa Ado Gwanja ‘Ga Gwanina’ sunan waƙar. Na je na yi wa Ado Gwanja, kuma ina ɗora ‘ɓoice’ ɗin sai mutanan studio suka yi ta cewa ai muryar ma kamar gwanjan, a nan ne aka yi ta bani shawarar gaskiya na cigaba da waƙa.

Ya farkon farawar ya kasance?

Gaskiya kam abun ba sauƙi yadda ake zaton sa, kafin kuma a saba.

Lokacin da ka yi waƙar a ina ka sake ta?

Babu, saboda lokacin ban san komai game da ‘Platform’ ba, balle na buɗe Youtube ko Audiomack ba, sai dai na bar ta a wayata.

Ka yi waƙoƙi sun kai kamar guda nawa?

Sun kai kamar guda Ashirin da biyar.

Wacce waƙa ce ta zama bakandamiyarka cikin waƙoƙinka?

Zankan ce, saboda idan aka sakata a wajan biki mata suna rawa sosai, da kuma yadda sunan waƙar ya zauna a bakin mutane.

Ko akwai wani ƙalubale da ka taɓa fuskanta game da waƙa?

Akwai oganniyata Hajjiya Rabi Zaria da ta haɗa ni da Aminu mai Dawayya suka zo har studio ɗin mu muka yi waƙa da shi, bayan ya gama ɗorawa naje na raka su mota, ina shigowa studio sai na ji ya fara salati wai waƙar ta bugu (Dariya) wannan shi ne ƙalubale da ba zan manta da shi ba.

Waɗanne irin nasarori ka samu game da waƙa?

Na samu nasarar riƙe kuɗin da ban taɓa riƙewa ba sanadiyyar waƙa, ina ma’amulla da mutanan da ban isa nayi ma’ammulla da su ba, sai ta sanadiyar waƙa.

Mu ɗan koma baya kaɗan, ka yi magana game da yadda ka sha gwagwarmayar haɗuwa da Ado Gwanja baka same shi ba tun farkon fara waƙar ka, shin a yanzu kun haɗu da juna ko kuwa tukunna dai?

Kafin haɗuwar dai akwai wani yaransa Musa Ubah wanda ya ba ni lamba, na yi taimasa magana a WhatsApp. Idan kuma nayi waƙa na tura masa to, ba ya yi min ‘reply’ sau ɗaya yayi min fatan alkhairi. A Kabuga akwai wani Shamsu Glo lokacin da ya ji waƙa ta a wajan wani sai ya kira ni a waya, na je muka haɗu sai yayi min alƙawari zai haɗa ni da Gwanja. Watarana suna aikin Ɗan Jarida a gidan Zoo sai ya ce in zo mu je ya kai ni gurinsa, muka je muka gaisa, na kunna masa waƙar ya ji muka yi hoto. To, tun daga ranar dai kamar ma ‘blocking’ ɗina yayi har zuwa yanzu ban sake ji ta kansa ba har yanzu.

Ya ka ɗauki waƙa a wajenka?

Waƙa sana’a ce babba, kuma hanyar aika saƙo mafi sauƙi.

Mene ne burinka na gaba game da waƙa?

Ina so na zama ɗaya daga cikin manyan mawaƙa a Africa in sha Allah.

Bayan waƙa kana wata sana’ar ne?

ina sana’ar ɗinki na maza da na mata.

A baya ka ce kana yin fim, kamar waɗanne irin finafinai ka fito a ciki?

Na fito a WATA SHIDA mun yi ‘scene’ da ADAM ZANGO, na fito a LAURE matsayin GOGA da MIJIN ABU. Wanda na fara kuma sunansa RASHIN UBA ni na fito a matsayin abokin jirumin. Akwai fim ɗin KICIMILLI SABON SALO wanda ni ne nayi waƙoƙin cikin fim ɗin har guda biyu kuma nayi ‘ɓideo’ a ciki.

Idan mutum yana so ya fara waƙa, ta ina zai fara?

Ya tsarkake niyarsa, ya tafi kansa tsaye Allah zai taimake shi, in sha Allah.

Wacce shawara za ka bawa masu ƙoƙarin fara waƙa?

Tsarkake kalamai, kada ka je garin neman ɗaukaka ka riƙa faɗar abin da bai kamata a ji ɗan’uwa bahaushe yana yi ko yana faɗa ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *