Jonathan Ya Gana Da Shugabannin PDP A Abuja Don Magance Rikicin Jam’iyyar

[ad_1]

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya yi wata ganawar sirri da shugabannin jam’iyyar PDP a Abuja.

An gudanar da taron ne a ofishin Jonathan da ke Maitama, Abuja, da yammacin ranar Talata.

  • 2027: Babu Wani Ɗan Takara Da Zai Haƙurar Ma Wani Takararsa A ADC – Atiku
  • AFCON 2025: Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Algeria A Wasan Kwata Fainal

Taron ya haɗa da mambobin Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NWC) na PDP, ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki (SAN), tare da wasu shugabannin jam’iyyar na jihohi.

Rahotanni sun nuna cewa ganawar na cikin jerin shawarwari da jam’iyyar ke nema daga manyan shugabanninta domin kawo ƙarshen rikicin da ya addabi PDP.

Tanimu Turaki da sauran shugabannin PDP sun isa ofishin Jonathan da misalin ƙarfe 6 na yamma.

Jam’iyyar PDP na fama da rikici tun bayan zaɓen fidda gwani na takarar shugaban ƙasa gabanin babban zaɓen shekarar 2023, wanda ya bai wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, tikitin yin takara a jam’iyyar.

Rikicin ya kuma taka rawa wajen shan kaye da jam’iyyar ta yi a zaɓen.

A halin yanzu, jam’iyyar ta kasu kashi biyu.

Tsagi ɗaya ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki, yayin da ɗaya tsagin ke ƙarƙashin Abdulrahman Muhammed.

Wannan tsagi na Abdulrahman Muhammed na biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *