CMG Ya Kammala Bitar Bikin Bazara Na 2026 Karo Na Hudu
[ad_1]
Yau Lahadi 8 ga wannan wata, babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin ko CMG a takaice ya kammala bitar shagulgulan bikin bazara na shekarar 2026 lami lafiya. Bayan kokarin da aka yi, nau’ikan shirye-shiryen da aka shirya sun kara kyautata, ‘yan wasa su ma sun kara cika da kuzari, ma’aikatan da abin ya shafa sun kara kwarewa kan ayyukansu. An lura cewa, daga kirkire-kirkiren al’adun gargajiyar kasar Sin, zuwa cudanyar al’adun Sin da waje, an isar da fatan alherin sabuwar shekarar Sinawa ta hanyar nuna shirye-shiryen bikin zuwa ga al’ummun fadin duniya baki daya. (Mai fassara: Jamila)
[ad_2]
Source link