An kama ’yan Najeriya 11 kan zargin amfani da soyayya suna damfarar matan Thailand

[ad_1]



An kama ’yan Najeriya 11 bayan jami’an ’yan sanda da na hukumar kula da shige da fice ta kasar Thailand sun bankado wata ƙungiyar masu amfani da soyayya don aikata damfara.

Kungiyar, mai mambobi 13, an kama mambobin nata ne a yankin Muang Thong Thani na kasar.

An gudanar da kamen a ranar Litinin, kuma kafar labarai kasar mai suna Labaran Thailand ta rawaito hakan a ranar Alhamis.

A cewar rahoton, bincike ya fara ne bayan wata ’yar Thailand ta shigar da ƙara a shekarar 2025, tana zargin cewa wani mai amfani da Facebook da ta yi soyayya da shi ya yaudare ta.

An ce wanda aka zarga ya yi ikirarin cewa shi injiniyan kasar China ne, ya kuma shawo kanta ta tura sama da kudin kasar baht miliyan biyu zuwa wani asusun zamba.

Rahoton ya ce: “Binciken ya fara ne bayan wata ’yar Thailand a Nong Khai ta shigar da ƙara a ƙarshen 2025, tana cewa an yaudare ta ta hanyar Facebook da Line ta wani da ya yi ikirarin injiniyan China ne mai suna ‘Bingwen Fu.’

“Bayan gina dangantakar soyayya, dan damfarar ya yi ikirarin cewa ba zai iya samun kuɗin da ake buƙata don aikin gini ba, ya kuma shawo kan wanda aka yaudara ta tura sama da baht miliyan biyu zuwa asusun zambar.

Rahoton ya ce bayan samun bayanan sirri, kwamishinan hukumar shige da fice, Pol Lt Gen Phanumas Boonyaluck, ya umarci a gudanar da aikin haɗin gwiwa, inda jami’ai suka gano wadanda ake zargi suna gudanar da zamba ta soyayya kai tsaye ta na’urorin lantarki.

An ƙara da cewa an kama mutane 13, ciki har da ’yan Najeriya 11 da ’yan Côte d’Ivoire biyu, a maboyarsu, inda wasu suka yi ƙoƙarin guduwa ba takalma amma aka cafke su.

“Mutane takwas daga cikinsu sun wuce lokacin izinin zama, yayin da aka gano ’yan Najeriya biyar sun shiga Thailand ba bisa ƙa’ida ba ta iyakar Laos.

Dukkansu za su fuskanci tuhumar laifin wuce izini da shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

Kamen ya zo kasa da mako guda bayan kama wani ɗan Najeriya a kasar bisa zargin laifin miyagun ƙwayoyi.

Aminiya ta rawaito cewa a ranar Litinin wani ɗan Najeriya mazaunin Thailand, Ukoma Jefta Nuzbech, ya shiga hannu bayan ya gudu daga shari’ar da ake yi masa kan rawar da ya taka a safarar miyagun ƙwayoyi a yankin Koh Pha Ngan na ƙasar.

A cewar rahoton, an fara kama wanda ake zargi a watan Maris 2025 bayan ya sayar da gram 25.71 na hodar Iblis ga wani ɗan sanda da ya ɓoye kansa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *