Ɗantsoho Ya Zayyana Nasarorin Da Tsarin e-Call Up System Ya Samar A Tashoshin Jiragen Ruwa

[ad_1]

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Ƙasa  NPA, ta ƙara nanata ƙudurinta, na ci gaba da yin amfani da tsarin fasahar zamani da a turance ake kira da, e-Call Up, domin ci gaba da magance cunkoson Jiragen Ruwa, a Tashohinta da ke a faɗin ƙasar.

Shugaban Hukumar Dakta Abubakar Ɗantsoho ne, ya bayar da wannan tabbacin a yayin da ya gabatar da wata ƙasida taron da ƙungiyar ƴan jarida mawallafa labaran fannin ta ƙasa, ta shirya.

Taken taron shi ne, dabarun yin amfai da kimiyyar zamani a ɓangaren fitar da kaya daga ƙasar da kuma shigo da su, cikin ƙasar

Taron wanda ya gudana a kwanan bayam an yi shi ne a otle ɗin De Marii da ke a jihar Legas.

Dakta Ɗantsoho, ya dantanta wannan tsarin wanda ake fi sani da ETO, a matsayin wata baabbar madafa, da ya samar da sauyi a fannin sufurin Jiragen Ruwa na ƙasar, musamman wajen samar da hanyoyin yin safara a Tashohin Jiragen Ruwa na Apapa da kuma ta Tin Can Island.

  • Yadda Tsare-tsaren Tinubu Na Fitar Da Kaya Ketare Suka Ƙara Wa NPA Ƙwarin Guiwa
  • Shugaba Tinubu Ya Karrama Shugaban NPA Da Lambar Yabo Ta Musamman

Shugaban wanda ya Manajan Darakta da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa na Hukumar Jimoh Anthony ya wakilce shi a wajen taron ya ci gaba da cewa, yin amfani da wannna fasahar a Tashohin Jiragen Ruwan, ya taimaka matuƙa, wajen magance cunkoson na Jiragen Ruwa da ke sauka a Tashohin ƙasar.

Ɗantsoho ya ci gaba da cewa, hakan ya kuma ƙara taimaka wa, wajen samar da sauƙin gudanar da hada-hada kuma a kan lokaci, ba tare da wata tangarɗa ba, da kuma ƙara bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan.

“Ayau wannan kimiyyar na samar da sauƙi wajen zirga-zirga, musamman a tsakanin manyan motoci da ke shiga da kuma fita daga cikin Tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar, “ Inji Shugaban.

A cewar shugaban samar da wannan fasahar zamanin, na daga cikin manyan nasarorin, da Hukumar ke tunƙaho da shi.

Ya ƙara da cewa, yin amfani da kimiyyar, ta kuma taimaka wajen magance dogon layi tare da kuma tabbatar da samar da kyakyawan yanyi da kuma gudanar da ayyukan Hukumar a cikin sauƙi.

Wani ƙarin cin nasarar ya haɗa da, kafa tsarin ganowa da kuma yin amfani da fasahar tsarin shige da fice, na manyan motocin.

Tsarin Shigar Manyan Motoci Tashoshin Na TTP:

Wannan kimiyyar za ta taimaka wajen kula da shige da kum aficen manyan motocin cikin Tashoshin Jiragen Ruwan da kuma magance cunksoson da ake samu a kan hanyoyi.

Dakta Ɗantsoho ya ƙara da cewa, fasahar ta taimaka wajen rage cunkson manyan motoci a Tashoshin Apapa da kuma ta Tin Can, inda yayi nuni da cewa, hakan ya nuna cewa, fasahar, na da matuƙar mahimmanci.

Shugaban ya ci gaba da cewa, bisa haɗakar da Hukumar ta yi da Hukumomin tsaro da kuma masu ruwa da tsaki, hakan ya ƙara taimaka wa wajen wanzar da tsarin tare da kuma magance cuinkson manyan motocin, wanda kuma hakan ke bai wa manyan motocin damar ajiye su, a wajen da ya dace.

A cewarsa, ci gaba da haɗakar da Hukumar ta NPA ke yi da masu ruwa da tsaki a fannin na sufurin Jiragen Ruwan ƙasar, hakan ya samar da nasara, wajen aiwatar da tsarin.

Kazalika, ya sanar da cewa, yin haɗaka da sauran ƙungiyoyin  ƙwadago da ke kula da wajejen ajiya manyan kaya a Tashar da kuma sauran Hukumomi, hakan ya ƙara taimaka wa tsarin, inda hakan ya kuma ƙara bunƙasa gudanar da ayyukan Hukumar a cikin nasara.

Da yake yin bayani kan ci gaban da aka samar a Hukumar ta NPA, Xantsho ya bayyana cewa, a kwanan baya, NPA ta gudanar da nazari a tsarin na E-Call Up, ya taimaka wajen toshe dukkan matsaloli da kuma ƙara ƙarfafa tsarin.

Ya sanar da cewa, ɗaya daga cikin sakamakon da aka samu shi ne, domin ƙara ƙarfafa bayar da tikiti, ga manyan motocin da ke shiga Tashoshin, ta hanyar amfani da tsarin na ETO.

A bisa ƙarƙashin tsarin na ETO, za a rinƙa sayen tikitin kai tsaye, musamman domin a toshe duk wata kafa, ta aikata almundana.

Kazalika, wani ƙarin ci gaban da aka samu shi ne, na samar da tsarin kimiyya a ƙofar shiga Tashoshin, domin karvar tiktin kai tsaye.

Hakazalika, tsarin zai ƙara rage cunkosn da kuma ƙara bunƙasa hada-hada a Tashohin.

Dakta Ɗantsoho ya ƙara jaddada cewa, tsarin na  e-Call Up wanda ya kasance na gaggawa ya taimaka wajen ƙara haɓaka ayyukan Hukumar ta NPA, ɗaukacin Tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar.

Ya bai wa masu ruwa da tsaki tabbacin cewa, a ƙarƙashin shugabancinsa, Hukumar ta NPA za ta ƙara mayar da hankali, wajen samar da sauye-sauye, musamman domin a ɗora kan wannan ci gaban da aka samar a Hukumar.

“Burin shi ne, mu taimaka wa ƙasar nan, na ƙoƙarinta na dogon zango na bunƙasa gasa a fannin a tsakanin ƙasashen duniya,” Inji Ɗantsoho.

A taron, ƙungiyarta kuma karrama Shugaban na Hukumar NPA, da lambar yabo ta MARCON kan irin ɗimbin nasarorin da ya samar a NPA.

Ƙungiyar ta sanar da cewa, Ɗantsoho, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen saita Tashoshin Jiragen Ruwa na ƙasar, inda hakan ya ƙara bunƙasa ayyukanta.

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta kuma karrama Janar Manaja na sashen dabarun sadawar na NPA Ikechukwu Onyemekara da lambar yabo ta yaɗa labarai.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *