Matashi ya kashe kishiyar kakarsa a Filato

[ad_1]



Ana zargin wani matashi mai shekaru 20, Ibrahim Mutari da hallaka abokiyar zaman kakarsa ta ɓangaren mahaifinsa, Hauwa Abubakar mai shekaru 70.

Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin da ya faru da misalin ƙarfe 3:00 na ranar Lahadin da ta gabata ya auku ne a garin Yanbula da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa Jihar Filato.

Mahaifin matashin da ake zargi, Abubakar Shuaibu, ya yi Allah-wadai da kisan yana mai bayyana aukuwar lamarin a matsayin muguwar nifaƙa.

Ya yi zargin cewa ɗan nasa ya kashe masa mata bayan maƙure mata wuya sannan ya soka mata wuƙa kuma ya kama gabansa.

Ita ma ’yar mamaciyar, Ummi Ahmed, ta zargi matashin da kashe mahaifiyarsu wanda ta ce tun kafin aukuwar lamari ya yi barazanar ɗaukar fansa kan rikicin da ya faru tsakaninsa da ɗan uwansu Musa a bara.

A cewarta, “Ibrahim da ƙanenmu Musa sun yi faɗa a bara, wanda a lokacin Musa ya soka masa wuƙa a ciki, aka garzaya da shi asibiti.

Sai dai ta ce a yayin da yake jinya, “Ibrahim ya yi rantsuwar cewa zai ɗauki fansa kan ’ya’yan mamaciyar ko ita kanta, kuma yau ya aiwatar da hakan.”

Ummi ta ƙara da cewa tun a wancan lokacin wata nas a asibitin ta gargaɗe su da su yi taka-tsantsan, saboda kalaman Ibrahim na da haɗari.

Ta bayyana cewa mamaciyar ce ke ta riƙa kula da shi a lokacin jinyarsa har aka sallame shi daga asibiti, “amma duk da irin ɗawainiya da ta yi ga shi yanzu ya kashe ta,” in ji Ummi.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Filato, SP Alabo Alfred wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, sai bai yi wani ƙarin haske a kai ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *