Majalisa ta yi watsi da zargin Amurka na yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya
[ad_1]
Majalisar Wakilai, ta yi watsi da zargin da Ƙasar Amurka, ta yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
Wannan martani na zuwa ne bayan wani Sanatan na Amurka, Ted Cruz, ya gabatar da ƙudirin doka a Majalisar Dattawan ƙasar, inda ya ce ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
A yayin gabatar da ƙudirin ya buƙaci a ƙaƙaba wa wasu jami’an Najeriya takunkumi.
Cruz ya ce: “ Ana kashe Kiristocin Najeriya saboda addininsu… lokaci ya yi da za a ɗauki mataki na gaske kan jami’an Najeriya da ke taimaka wa irin waɗannan ayyuka.”
Sai dai ’yan majalisar Najeriya sun yi watsi da wannan batu.
Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu, ya ce wannan iƙirarin ba gaskiya ba ne game da halin da Najeriya ke ciki.
“Matsalar tsaro a Najeriya tana da yawa, ta’addanci, ‘yan fashi, rikicin manoma da makiyaya, kuma tana shafar mutane na kowane addini,” in ji Kalu.
“Ba daidai ba ne a fassara waɗannan matsaloli a matsayin hare-haren da gwamnati ke kai wa addini ɗaya ba.”
Majalisar ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aike wa Amurka mar6a hukumance, tare da tattaunawa don fahimtar juna kan wannan lamari.
Haka kuma, ’yan majalisar sun buƙaci a gaggauta naɗa jakadun Najeriya a Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, shi ma ya yi watsi da zargin Cruz, inda ya ce “ba gaskiya ba ne kuma babu wata hujja da ta tabbatar da hakan.”
“Ba gaskiya ba ne cewa an ƙome coci sama da 20,000 ko kuma an kashe Kiristoci 52,000,” in ji shi.
“Najeriya ƙasa ce mai addinai da dama. Babu wani jami’in gwamnati da zai goyi bayan tashin hankali a kan addini.”
Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta tabbatar da cewa an kai wa wasu Kiristoci hare-hare, amma ta ce matsalar tana shafar kowa, don haka gwamnati ta tabbatar da adalci.
“Kiristoci da dama sun rasa rayukansu a wuraren ibada,” in ji Archbishop Daniel Okoh, shugaban CAN.
“Muna kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su kare raykan dukkanin ‘yan ƙasa baki ɗaya, kuma a hukunta masu laifi.”
Majalisar ta jaddada cewa Najeriya na da ’yancin yin addini kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, tare da kira ga haɗin kai da fahimtar juna don kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ke shafar kowa.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link