An Nuna Shagalin CMG Na Murnar Bikin Bazara A Jiragen Kasa Na Nijeriya
Kwanan nan, a karon farko, an nuna shirye-shiryen shagalin da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya shirya don murnar bikin bazara, ta akwatunan talabijin da ke cikin jiragen kasa masu zirga-zirga a tsakanin biranen Lagos da Ibadan, da ma na cikin birnin Abuja.
Shirye-shirye masu kayatarwa na shagalin sun jawo hankulan fasinjoji masu yawa, wadanda suka bayyana cewa, shirye-shiryen sun burge su matuka, wadanda suka kara fahimtar da su game da yadda al’ummar Sinawa ke murnar sabuwar shekarar gargajiyarsu da ma al’adun da ke tattare da bikin. Wasunsu kuma suka bayyana sha’awarsu game da shirin yadda mutum-mutumin inji tare da yara suka gabatar da wasan Kungfu, ganin yadda al’adar gargajiya ta hadu da fasahar zamani.
Kamfanin CCECC na kasar Sin ne ya gina layin dogo da ke tsakanin Lagos da Ibadan da kuma na cikin birnin Abuja. Titin jirgin kasa na Lagos zuwa Ibadan da ke Nijeriya, tagwayen layin dogo na farko ne da aka gina bisa ma’aunin inganci na kasar Sin a yammacin Afirka, kuma titin jirgin kasa na cikin Abuja ya kasance irinsa na farko a shiyyar ta yammacin Afirka. (Lubabatu Lei)