Sabbin Nau’o’in Masana’antun Ba Da Hidimomi Suna Karuwa

[ad_1]

Jiragen kasa na yawon bude ido masu dadi, jiragen ruwa dauke da fasinjoji masu inganci, ayyukan tsaftace gida masu inganci… Duk wadannan ana shirya su!

A ranar 6 ga wata, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar Sin ya gudanar da taron tattauna manufofi na yau da kullum don gabatar da matakan da suke da alaka da habaka sabbin nau’o’in masana’antun ba da hidimomi. Wadannan matakan sun bawa kamfanonin kasashen waje da suka yi kasuwanci a Sin damammaki masu kyau.

A wannan shekarar, ana cika shekaru 10 da kasancewar kamfanin Viking Cruises a Sin. Bayan ganin “habaka sabbin hanyoyin amfani da jiragen ruwa dauke da fasinjoji da kuma inganta matsayin ba da hidima na jiragen ruwa” a cikin tsarin aiki da abin ya shafa, an karfafa wa kamfanin gwiwa sosai.(Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *