Kotu Ta Ƙi Amincewa Da Bukatar Tsoffin Kwamishinonin Kano Na Riƙe Motocin Gwamnati
[ad_1]
Babbar kotun masana’antu reshen shari’a na Kano, a ranar Litinin ta yi watsi da bukatun gaggawa da tsoffin mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano suka shigar, inda suke neman a hana gwamnatin jihar karɓe motocin gwamnati da aka ba su yayin da suke kan muƙami.
An haɗa bukatun, waɗanda suke da manufa iri ɗaya, kuma aka saurare su a gaban Mai shari’a Mahmood Abba Namtari a ranar Litinin.
- Kasar Sin Za Ta Yi Aiki Da Sauran Kasashe Wajen Karfafa Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya
- Matatar Dangote Ta Ƙara Farashin Fetur, Ta Dakatar Da Lodi
A cikin taƙaitaccen hukuncin, kotun ta ƙi bayar da umarnin wucin-gadi da masu ƙarar suka nema.
Daga bisani, an ɗage shari’un zuwa ranar 10 ga Maris, 2026, domin ci gaba da sauraro.
Tsoffin kwamishinonin da abin ya shafa sun haɗa da Yusuf Kofar-Mata, tsohon Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire; Ibrahim Umar, tsohon Kwamishinan Tsaron Cikin Gida; Nasir Garo, tsohon Kwamishinan Ayyuka na Musamman; Adamu Aliyu Kibiya, tsohon Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci; da Mustapha Kwankwaso, tsohon Kwamishinan Matasa.
A cikin ƙarar da suka shigar, masu ƙarar sun lissafa Babban Lauyan Jihar Kano, Gwamnan Jihar Kano, da Hukumar Karɓar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano a matsayin waɗanda ake ƙara.
Suraj Sa’ed (SAN) ne ya jagoranci tawagar lauyoyi biyar da suka wakilci tsoffin kwamishinonin, waɗanda suka haɗa da Mukhtar Sani Daneji, Dalhatu Yusuf Dada, Yusif Mu’azu Sani, Auwal Adam Ibrahim da Muhammad Uba Yakubu.
[ad_2]
Source link