Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil
[ad_1]
Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakin firaministan gwamnatin kasar, Ding Xuexiang, ya halarci taron koli na bangarorin da suka kulla yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya karo na 30, wato COP30 a takaice, a birnin Belem na kasar Brazil.
Yayin taron na jiya Alhamis 6 ga wata, Ding ya gabatar da jawabi, wanda a cikinsa ya ce a bana ake cika shekaru 10 da kulla Yarjejeniyar Paris, kana aikin daidaita yanayin duniya ya shiga wani mataki mai muhimmanci. A cewar Ding, kasar Sin ta samu sakamako mai gamsuwa a fannin cika alkawuran da ta dauka na takaita fitar da iska mai dumama yanayi, kana kasar za ta gaggauta sauya tsare-tsaren tattalin arzikinta zuwa irin na kare muhalli, da kokarin samar da karin gudummawa ta fuskar tinkarar sauyawar yanayin duniya.
Ban da haka, babban jami’in ya ba da wasu shawarwari guda 3 ga dukkan mahalarta taron, wadanda suka hada da, na farko, a karfafa imani wajen dosar alkibla mai dacewa, da neman samun ci gaba a dukkan bangarori kare muhalli, da raya tattalin arziki, da samar da guraben aikin yi, da rage talauci, da dai sauransu. Na biyu kuma, a aiwatar da yarjeniyoyin da aka kulla a baya, da sanya kasashe masu sukuni su rika sauke nauyin takaita fitar da hayaki mai dumama yanayi, da cika alkawarinsu na tallafa wa kasashe masu tasowa. Kana shawara ta uku da Mista Ding ya gabatar ita ce, a karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban, don samar da wani nagartaccen muhallin aiwatar da hadin kai a bangarorin tattalin arziki da ciniki, da tabbatar da cinikin kayayyaki masu ba da damar kare muhalli cikin ‘yanci, don biyan bukatun dake akwai a duniya na samun ci gaban al’umma mai dorewa.
Bugu da kari, a gefen taron na COP30, Ding ya gana da sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Mista Antonio Guterres. (Bello Wang)
[ad_2]
Source link