Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano

[ad_1]



Wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Danjuma Salman, ya rasu bayan ya faɗa cikin rijiya a Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Gwale.

Rahotanni sun nuna cewa yaron ya zame ne sannan ya faɗa cikin rijiyar wadda murfinta ya lalace.

Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:05 na safe daga wani mai suna Saminu Dayyabu, wanda ya sanar da su cewa wani yaro ya faɗa cikin rijiyar.

“A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, sun tarar da yaro ɗan shekara biyu, Danjuma Salman, wanda ya faɗa cikin wata rijiya da murfinta ya lalace,” in ji sanarwar.

Abdullahi, ya ce jami’an hukumar sun fito da yaron, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.

An miƙa gawar yaron ga mahaifinsa, Salman Dayyabu, bayan an fito da shi daga rijiyar.

Daraktan Hukumar Kashe Gobara na jihar, Alhaji Sani Anas, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyayen yaron.

Ya kuma yi kira ga mazauna unguwanni da su riƙa rufe rijiyoyi da sauran wuraren ruwa yadda ya kamata domin guje wa irin wannan iftila’i.

Haka kuma ya shawarci iyaye da su riƙa kula da yaransu sosai, musamman a wuraren da ke da hatsari.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *