Har yanzu ganin komawar Abba APC nake kamar a mafarki – Kwankwaso
[ad_1]
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana baƙin cikinsa kan ficewar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, inda ya bayyana hakan a matsayin babban butulci.
A cikin wata hira ta musamman da BBC Hausa ta yi da shi, Kwankwaso ya bayyana ficewar Gwamnan daga NNPP a matsayin abin mamaki da har yanzu yake ɗaure masa kai.
Kwankwaso, wanda ya kasance jagora kuma ubangidan siyasar Gwamnan tsawon shekaru 40, ya ce labarin ficewar ya zo masa fiye da yadda ya zata. Ya ce har yanzu ya kasa gasgata abin da idonsa ya gani.
Ya ce: “Abin da ya faru a Kano babban abin bakin ciki ne da takaici. Wani lokaci idan na tashi daga barci sai in ɗauka mafarki ne, amma gaskiyar ita ce ya bar NNPP ya koma APC.”
Tsohon Gwamnan na Kano ya kuma ce sauya sheƙar zuwa APC ba kawai sauyin siyasa ba ne, illa barin alaƙar da suka gina tsawon shekaru 40.
Ga yawancin ’yan Najeriya, dangantakar Kwankwaso da “Abba Gida-Gida” ta kasance ɗaya daga cikin mafi ƙarfi a tsarin siyasar yaro da ubangida.
Ya ce: “Abin da ya fi zafi shi ne dangantakarmu ta fiye da shekaru 40. Bayan barinmu zuwa ‘Gandujiyya’, na kan tsaya in tambayi kaina: Me ya faru? Wane ne ya yi kuskure? Ni ne, jam’iyya ce, ko mambobinta? Ba ni da amsa.”
Kwankwaso ya kuma yi watsi da hujjar Gwamna Abba cewa NNPP na fama da rikicin cikin gida. Ya ce NNPP ita ce jam’iyya mafi kwanciyar hankali a Najeriya.
Ya ce: “Babu gaskiya a ikirarin cewa akwai rikici a NNPP. Ina tabbatar muku babu rikici, ku jira tarurrukan su, nan ne za ku ga rikici na gaskiya.”
A cikin gargadi ga waɗanda suka bi Gwamnan zuwa APC, Kwankwaso ya ce za su ƙare da nadama cikin tsarin Ganduje kuma su rasa asalin siyasar su.
Ya ce: “Duk wanda ya bar mu, ya cire kar hula kuma ya koma cikin ‘Gandujiyya’ ya tafka kuskure. Yadda jama’a ke kallon Ganduje shi ne yadda za su fara kallon Abba. Lokacin da Ganduje ya ɗaga hannun Abba, Abba ya faɗi zaɓe.”
Kwankwaso ya ƙara da cewa ba zai amfani da tashin hankali ba, amma “cin amanar” kujerar da jama’a suka bayar da rayuka da dukiyarsu domin kare ta ba za a manta da ita ba.
Ya ce: “Lokaci zai bayyana gaskiya. Ko da bai dawo gare mu ba, wata rana zai yi nadamar wannan matakin da ya ɗauka.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link