Tinubu ya tafi Turai hutu kafin halartar taron Abu Dhabi
[ad_1]
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bar Legas zuwa Turai domin ci gaba da hutun ƙarshen shekara, gabanin tafiyarsa zuwa Birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).
Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan Harkokin Watsa Labarai, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu zai tafi Abu Dhabi ne, bisa gayyatar Shugaban UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, domin halartar taron ‘Abu Dhabi Sustainability Week Summit 2026’ da aka shirya gudanarwa a watan Janairu.
Za a yi taron na tsawon mako guda, kuma ana shirya shi kowace shekara domin haɗa shugabanni daga gwamnatoci, kasuwanci da ƙungiyoyin al’umma, don tattauna samar da hanyoyin ci gaban duniya.
Taken taron na wannan shekara an masa taken: “The Nexus of Next: All Systems Go,”.
Zai mayar da hankali kan sauya ra’ayoyi zuwa aikace-aikace a fannoni kamar ƙirƙire-ƙirƙire, kuɗi da bunƙasar ɗan Adam, tare da inganta manufofin ɗorewar ci gaban duniya.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala taron.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link