’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Sace Limami Da Wasu Mutane 7 A Filato
[ad_1]
’Yan bindiga sun kai hari yankin Dogon Ruwa da ke gundumar Bashar a Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato, da yammacin ranar Lahadi, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wasu mutum takwas.
Daga cikin waɗanda aka sace akwai wani limami, ladani, da kuma wasu mazauna yankin guda shida.
An kai musu harin ne yayin da suke aiki a wajen garin lokacin suke haɗa gawayi domin sayarwa.
Wani shugaban matasa a yankin, Shapi’i Sambo, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa harin ya jefa tsoro a zukatan mazauna yankin.
Ya ce ’yan bindigar sun bayyana ba zato ba tsammani, inda suka sace mutanen.
Mazauna yankin sun ce sun bi sahun maharan, amma ba su samu nasarar ganinsu ba saboda dare ya yi.
An tura jami’an tsaro zuwa yankin domin tsaurara tsaro, kuma an shawarci jama’a da su kwantar da hankalinsu.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto rundunar ’yansandan Jihar Filato ba ta fitar da wata sanarwa ba.
Al’ummar Dogon Ruwa dai sun fuskanci hare-haren ’yan bindiga a baya, inda aka kashe sojoji, ’yan banga da kuma fararen hula.
[ad_2]
Source link