An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Na “Sin a Yanayin Bazara” A Afirka Ta Kudu Da Jamus

[ad_1]

Babban rukunin gidan rediyo da talibijin kasar Sin wato CMG, ya gudanar da taron tattaunawa na duniya na “Sin a yanayin bazara: ci gaban Sin, dama ga duniya” a ranar Talata a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu. Kuma shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.

Cikin jawabin nasa Shen Haixiong ya bayyana cewa, tarukan majalisun NPC da CPPCC na kasar Sin, a matsayinsu na muhimmiyar tagar kallon kasar a sabon zamani, sun sake jawo hankalin duniya. Tarukan na bana sun zartas da muhimman takardu, kamar tsarin shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15.

Kazalika, tsarin ci gaba mai inganci na Sin ya kuma ba da sabbin jerin damammaki ga duniya. Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada a lokacin wadannan taruka 2 cewa, ya kamata a kara bude kasuwar Sin ga ketare, da kuma fadada kasuwannin duniya, wanda hakan ya sake nuna cikakkiyar niyyar kasar ta “bude kofarta ga ketare bisa iyakacin kokarinta”.

Shen Haixiong, ya kuma yi fatan CMG za ta yi amfani da karfinsa na kasancewar kafar watsa labarai ta zamani, dake sahun gaba a duniya mai hade fifikon yada labarai da kirkire-kirkire na fasaha, da kuma albarkatun kafafen yada labarai, wajen inganta sakamakon tsarin zamanantar da al’ummar Sin ta yadda zai fi amfanar da duniya baki daya.

Ban da haka, a dai ranar ta Talata, kamfanin CMG ya gudanar da irin wannan taro a Jamus, tare da babban ofishin jakadancin Sin dake Düsseldorf, babban birnin jihar North Rhine-Westphalia. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *