Mutanen Kurmin Wali Sun Yabawa Gwamna Sani Kan Alƙawarin Kuɓutar Da ‘Yan Uwnansu
[ad_1]
Kwanaki hudu bayan kai hari a garin Kurmin Wali da ke karamar hukumar Kajuru a Jihar Kaduna wasu Wadanda harin ya rutsa dasu sun fara bayyana irin mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki, tare da jaddada kwarin gwiwa ga jagorancin Gwamna Uba Sani.
Daya daga cikin wadanda suka tsira, Mista Joseph, ya ce maharan sun kai farmaki cikin al’ummar a safiyar Lahadi yayin da jama’a ke cikin ibada. Ya bayyana cewa maharan sun umurci masu ibadar da su kwanta rubda ciki kafin su tilasta musu zuwa wani daji da ke kusa.
A wata zantawa da manema labarai wadanda suka tsiran Sun kuma jadadda kwarin gwaiwarsu dangane da kokarin gwamnan jihar kaduna Uba Sani.
A cewarsa, ya samu damar tserewa ne a lokacin da rikici ya barke, sannan daga bisani ya samu ya tsira ya isa wuri mai aminci.
Duk da mummunan abin da ya faru, Mista Joseph ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda ya kai ziyara Kurmin Wali da kansa domin jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da tantance halin da ake ciki. Ya bayyana jagorancin gwamnan a matsayin na tausayi da kula da jin dadin al’umma.
Ya kara da nuna kwarin gwiwa ga kudurin gwamnan wajen tabbatar da tsaro da walwalar mazauna jihar, tare da yi masa addu’ar samun nasara da ci gaba da jagoranci nagari.
A halin da ake ciki kuma, majiyoyi sun tabbatar da cewa an kwashe wadanda harin ya rutsa da su zuwa Kaduna domin samun kulawar lafiya da tallafin shawarwari na kwakwalwa, bisa ga alkawurran da Gwamna Uba Sani ya bayar a lokacin ziyararsa zuwa yankin.
[ad_2]
Source link