Kotu ta tura Malami da matarsa zuwa Gidan Yarin Kuje

[ad_1]



Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta aike ta tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami da matsarsa zuwa Gidan Gyarin Hali da ke Kuje.

A ranar Talata Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin tura Malami da matsarsa Asabe Bashir da kuma dansa Abdulaziz zuwa Gidan Gyaran Hali na Kuje, bayan ta yi watsi da bukatar belin su.

Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) ce ta gurfanar Malami da matar tasa da dansa ne, bisa zargin su da laifuka 16 safarar kudaden haram.

Asabe ma’aikaciya ce a wani kamfani mai suna Rahamaniyya Properties Ltd, wanda ke da alaka da Malami.

Kotun ta sa a tsare su a gidan yari ne bayan dukkansu sun ki amsa laifukan da EFCC take tuhumarsu da aikatawa.

EFCC ta zarge su da gudanar da wasu hadahadar kudade da zummar boye inda aka samo biliyoyin kudaden ta hanyar amfani da asusun banki daban-daban da kuma sayen kadarori a jihohin Abuja, Kano da  Kebbi.

Hukumar ta ce an yi haka ne daga shekarar 2015 zuwa 2025, wanda ya hada da shekara 8 da Malami ya yi aiki a mastayin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a a zamanin tsohon Shugaban Kasa, Marigayi Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2023.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *