’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum da ake zargin ɗan bindiga ne da ke aiki tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru.
Rundunar ta kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai 80 da wasu tarin makamai.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa wanda aka kama, Adamu Adamu, mai shekaru 30, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Song a Jihar Adamawa.
Amma wanda aka kama mazaunin unguwar Jauro Jatau da ke Akko, Jihar Gombe.
An kama shi ne ranar 4 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihan bayanai da suka nuna cewa yana tare da wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke aiki a tsakanin Najeriya da Kamaru.
A yayin wani samame da CSP Ali Madaki ya jagoranta a ƙarƙashin Operation Hattara, rundunar ta gano inda suka ɓoye makamai a wani tsauni da ke kusa da ƙauyen Wuro Biriji a Jihar Adamawa.
Rundunar ta ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biy, harsasai 80, gidan harsasai bakwai, sarƙoƙi, makulli, wuƙa da ƙananan jakunkuna huɗu.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar, CP Bello Yahaya, ya yaba wa jami’in wajen kama wanda ake zargin.
Ya kuma jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da yaƙi da masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.
Ya buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro bayanai domin tabbatar da zaman lafiya a Gombe da sauran maƙwabtan jihohi.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link